Shugaba Tinubu Ya Roƙi Yan Najeriya Muhimmin Abu 1 da Zai Taimaka Wajen Yaƙar Ta'addanci a Arewa

Shugaba Tinubu Ya Roƙi Yan Najeriya Muhimmin Abu 1 da Zai Taimaka Wajen Yaƙar Ta'addanci a Arewa

  • Bola Ahmed Tinubu ya roƙi dukkan yan Najeriya su ba shi haɗin a kokarin yaƙi da ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya da tsaro
  • Shugaban ƙasar ya nemi wannan alfarma ne yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Jumu'a
  • Ya ce Arewa maso Gabas ta jima tana fama da hare-haren ƴan tada ƙayar baya amma idan aka haɗa kai duk wani duhu zai yaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ɗaukacin ƴan Najeriya su haɗa kai wuri ɗaya wajen yaƙi da ta'addanci da samar da zaman lafiya da tsaro.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Roki Yan Najeriya Su Hada Kai Wajen Yaki da Ta'addanci Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya yi wannan roko ne a wurin kaddamar da wani littafi kan ayyukan ta'addanci a Arewa maso Gabas wanda ya gudana a Abuja ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana hanya 1 da za a magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas

Rundunar sojin saman Najeriya ce ta rubuta littafin tare da haɗin gwuiwar jami'ar Babcock, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu, wanda shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya wakilta, ya ce:

"Mu tashi tsaye mu haɗa kai a yaki da ta'addanci tare da yin aiki don samar da zaman lafiya, tsaro da wadata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, a Najeriya da sauran kasashen duniya."

Da yake tsokaci kan littafin, shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, "yana wakiltar babbar gudummawa wajen fahimtar daya daga cikin manyan kalubalen zamaninmu, yaki da ta'addanci."

Yadda zamu magance ta'addancu a arewa - Tinubu

Shugaban ya ce yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya dade yana fama da matsalar ta’addanci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya kara da cewa munanan hare-haren da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi suka rika kaiwa ya jefa mutanen yankin da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma Najeriya gaba daya cikin ƙunci.

Kara karanta wannan

"Ban san laifi bane" Abdulazeez wanda ya ƙona Alƙur'ani a Arewa ya aike da saƙo ga Musulman Najeriya

Ya ci gaba da cewa:

"Duk da haka akwai fata, fatan cewa idan muka fahimci yanayin tare da haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki zamu shawo kan waɗannan kalubalale mu dawo da zaman lafiya a shiyyar."

Hatsarin jirgin ya yi ajalin mutum 10

A wani rahoton kuma Mummunan hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutane 10 a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) ce ta tabbatar da haka, ta ce Kwale-Kwalen na ɗauki mutum 34 lokacin da haɗarin ya afku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262