Yajin Aikin NLC Ya Kawo Cikas a Shari'ar Tsohon Gwamnan CBN Emefiele

Yajin Aikin NLC Ya Kawo Cikas a Shari'ar Tsohon Gwamnan CBN Emefiele

  • Yajin aikin ƙungiyar JASUN ya dakatar da shirin sake gurfanar da tsohon Gwamnan CBN a gaban babbar Kotun Abuja
  • Kungiyar ma'aikatan shari'a ta umarci mambobinta su bi umarnin NLC su shiga yajin aikin sai baba ta gani
  • Wannan lamari dai ya kawo tsaiko a shari'ar Emefiele, wanda aka tsara ci gaba yau Laraba, 15 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An samu tsaiko a shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda za a gurfanar a gaban babbar kotun babban birnin tarayya Abuja.

Tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Yajin Aikin NLC Ya Kawo Cikas a Shari'ar Tsohon Gwamnan CBN Emefiele Hoto: Mr Godwin Emefiele
Asali: Getty Images

Hakan ya faru ne sakamakon yajin aikin da ƙungiyar ma'aikatan shari'a (JUSUN) ta shiga a reshenta na babbar Kotun Abuja bisa umarnin ƙungiyar kwadago NLC.

Kara karanta wannan

Yanzu: Majalisar dattawa ta tsoma baki kan yajin aikin ƙungiyoyin kwadago, ta ɗauki matsaya 1 tak

JUSUN ta umarci baki ɗaya mambobinta su bi sahun shiga yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ma'aikata NLC da TUC suka ayyana wanda aka fara ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikata sun fara wannan yajin aikin na sai baba ta gani a faɗin Najeriya kan cin mutuncin da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a jihar Imo ranar 1 ga watan Nuwamba, 2023.

Yadda aka samu tsaiko a shari'ar Emefiele

Yayin da wakilin Channels tv ya ziyarci harabar Kotun ranar Laraba, ya ga ƙofar shiga a rufe kuma babu alamun lauyoyi na kai kawo a cikin Kotun.

Idan baku manta ba, a makon jiya ne mai shari'a Olukayode Adeniyi na babbar Kotun Abuja ya ba da belin tsohon Gwamnan CBN, Mista Emefiele.

Ya kuma bada umarnin a sake shi nan take ya koma hannun lauyoyinsa, waɗanda ya ɗora musu alhakin gabatar da shi a gaban Kotun yau Laraba.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: "Mun kama waɗanda suka jibgi shugaban NLC" NSA ya aike da sako ga kungiyoyin kwadago

Sai dai a halin yanzu, sake gurfanar da Emefiele ya gamu da cikas saboda yajin aikin da ma'aikata ke yi, wanda ya shafi ɓangaren shari'a, rahoton Guardian.

Mista Emefiele ya fara fuskantar matsaloli ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da shi daga matsayin Gwamnan CBN ranar 9 ga watan Yuni, 2023.

Barista Tukur Badamasi, wani lauya mai zaman kansa a Kaduna ya faɗa wa Legit Hausa cewa wannan matsala ce da ta faru ba tare da tsammani ba, ba wanda za a ɗora wa laifi.

"Irin wannan batu na yajin aiki ya shafi kowa, lauyoyin Emefiele da ma'aikatan kotu kowa ta shafe shi, don haka ba wanda ya yi laifin rashin sake gurfanar da shi."
"Idan aka janye yajin aiki, Kotu zata sake nazari ta sanya sabuwar rana kuma ta aika wa kowane ɓangare, to idan ba su kawo shi bane za a ce sun yi laifi," in ji shi.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

BUK, Bankuna da Wasu Makarantu Sun Shiga Yajin Aiki

A wani rahoton na daban kun ji cewa Abubuwan sun tsaya cik a a ɓangaren makarantu da ma'aikatun Gwamnati a Kano bayan fara yajin aikin NLC da TUC.

Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantun Firamare, sakandire da manyan makarantu harda BUK ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel