BUK, Bankuna da Wasu Makarantu Sun Shiga Yajin Aiki, Gwamnatin Abba Ta Dakatar da Muhimmin Abu 1

BUK, Bankuna da Wasu Makarantu Sun Shiga Yajin Aiki, Gwamnatin Abba Ta Dakatar da Muhimmin Abu 1

  • Abubuwan sun tsaya cik a a ɓangaren makarantu da ma'aikatun Gwamnati a Kano bayan fara yajin aikin NLC da TUC
  • Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantun Firamare, sakandire da manyan makarantu harda BUK ranar Talata
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sanar da ɗage jarabawar tantance ɗaliban da zasu zana jarabawar kammala sakandire saboda yajin aikin

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ƙungiyar ma'aikatan gwamnati reshen jihar Kano (NLC) ta bi sahun fara yajin aikin sai baba ta gani domin biyayya ga umarnin ƙungiyar ta ƙasa.

Yajin aiki ya kankama a Kano.
An Garkame Bankuna da Makarantu a Kano, Gwamnatin Abba Ta Dakatar da Abu 1 Hoto: NLC
Asali: UGC

Wakilin jaridar Punch wanda ya sa ido kan lamarin, ya gano cewa makarantun Firamare da Sakandire, har da manyan makarantu sun bi sahun shiga yajin aikin yau Talata a Kano.

Kara karanta wannan

Yajin aiiki: Abu ya girmama, Ma'aikata sun sha mamaki yayin da suka fita wurin aiki a jihar Arewa

An rufe makarantu, ɗaliban BUK sun koka

An fahimci cewa ɗaliban Firamare da na makarantun Sakandiren jeka ka dawo da suka tafi makaranta tun ƙarfe 7:30 na safe, dole suka koma gida saboda babu malami ko ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma wannan yajin aiki ya shafi ayyukan bankuna, asibitoci da sauran ma'aikatun gwamnati a cikin kwaryar birnin Kano.

Sakateriyar Audu Baƙo da ke tattare da mafi akasarin ma'aikatun Gwamnati, an kulle ta baki ɗaya sakamakon fara yajin aikin ma'aikata.

Duk da wasu ma'aikata waɗanda ake kyautata zaton ba su samu labarin shiga yajin aikin ba, sun fita wurin aiki amma bisa tilas suka koma gidajensu daga baya.

Daliban Jami’ar Bayero Kano da ke zana jarabawar zango na farko, yajin aikin ya shafe su saboda da dama daga cikin su da suka je dakin jarrabawa ba su ga kowa ba, haka suka koma ɗakunan su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukuma a jihar Arewa

“Dalibai da dama da za su zana jarabawa da safe sun koma ɗakunan su cikin bacin rai saboda ba su ga kowa a dakin jarabawar ba," in ji wata ɗaliba.

Gwamnati ta dakatar da jarabawa

Bugu da ƙari, ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta dakatar da jarabawar tantance maasu zana jarabawar fita sakandire ta 2023 da aka shirya gudanarwa a yau sai nan gaba.

A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ɗauke da sa hannun Daraktan hulɗa da jama'a, Balarabe Kiru, ya ce an ɗauki matakin saboda yajin aikin da NLC da TUC suka shiga.

Wani Malamin makaranta a Hotoro, cikin birnin Kano, Sanusi Isiyaku, ya shaida wa Legit Hausa cewa bai je makaranta ba saboda yajin aikin NLC.

"Mafi yawan Malamai ba su je makaranta ba, wasu kalilan sun je kuma sun sanar da ɗaliban da suka je cewa babu makaranta saboda yajin aiki."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar APC ya rantse da Allah, ya ce zasu tuhumi Tinubu kan yadda aka yi da kuɗin tallafin fetur

A cewarsa, ya ga wasu ma'aikatan Gwamnati da ya sani a unguwarsu duk ba su fita aiki ba yau, kuma duk ba zai rasa nasaba da batun yajin aikin ƙungiyar kwadago ba.

NLC ta kulle ma'aikatu a jihar Filato

A wani rahoton na daban kuma Kungiyar ma'aikatan Najeriya ta hana ma'aikatan jihar Filato da na.tarayya shiga wuraren aikinsu ranar Talata a Jos.

Ma'aikatan sun ga abin mamaki yayin da suka tarad da mambobin NLC sun kewaye ofisoshinsu, sun basu umarnin su koma gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel