Tinubu Ya Yi Alkawarin Karawa Sarakuna Karfi, Za a Ba Su Matsayi a Tsarin Mulki

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karawa Sarakuna Karfi, Za a Ba Su Matsayi a Tsarin Mulki

  • Bola Ahmed Tinubu zai karfafi sarakunan gargajiya ta hanyar rataya masu nauyi a karkashin kundin tsarin mulki na kasa
  • Shugaban Najeriya ya ce zai bi ta hannun ‘majalisa, ayi wa dokar kasa kwaskwarima domin a tafi da Sarakuna a mulki
  • Mai girma Bola Tinubu ya daukan ma kan shi wannan alkawari ne wajen bikin taya Sarkin Ondo cika shekaru 70 da haihuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dauki alkawari cewa gwamnatinsa za ta karawa Sarakunan gargajiya karfi a dokar kasa.

Daily Trust ta rahoto cewa Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi aiki da ‘yan majalisar tarayya domin a ba Sarakuna aiki a tsarin mulki.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai ba Sarakuna iko Hoto: @el_bonga
Asali: Twitter

Tinubu ya taya Sarkin Ondo murnar cika 70

Kara karanta wannan

Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

Shugaban Najeriyan ya dauki wannan alwashi ne wajen taya Mai martaba Oba Victor Kiladejo murnar cika shekara 70 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadi Sarkin Ondo ya yi bikin murnar kara shekara, aka shirya biki a wani coci na Cathedral Church of St. Stephen a Ondo.

Minista ya wakilci Bola Tinubu

Shugaban Najeriya ya samu wakilcin Ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo zuwa wannan biki da aka shirya a jiya.

Da yake jawabi da yawun shugaban kasa, Tunji-Ojo ya jaddadawa Sarakunan gargajiya cewa gwamnati mai-ci za ta yi aiki da su.

Rahoton ya ce Gwamnatin Tinubu ta na ganin Sarakunan gargajiya suna da rawar talawa wajen kawo tsaro da zaman lafiya a kasarsu.

Haka zalika nauyin kare al’adar gargajiya ta rataya ne a kan wadannan Sarakunan kasar.

Sarki Kiladejo ya yabawa Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da mukarrabansa sun daura haramar yin Umrah a ziyararsu ta Saudiyya

Mai martaba Oba Kiladejo ya ji dadin yadda Bola Tinubu ya tuna da shi, har ya aiko wakili domin ya wakilce shi a wajen wannan biki.

Gudumuwar Sarakuna a gwamnati

Leadership ta ce Gwamna Rotimi Akeredolu ya taya Sarkin murna, ya yi bayanin yadda yake taimakawa gwamnatinsa da shawarwari.

Rotimi Akeredolu ya ce Sarki Kiladejo ya bada gudumuwa wajen kawo cigaban al’umma.

Shugaban INEC ya sabawa kotu?

Ku na da labari Kotu ta ce a daina daukar Victor Oye a matsayin shugaban APGA, amma ana zargin hukumar INEC ta nuna kunnen kashi.

Edozie Njoku ya ja-kunnen shugaban INEC da shugabannin jam’iyyar APGA a kan sabawa kotu, ya ce yin hakan zai kai su gidan gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel