Manyan Sarakuna 5 da za su taka rawar gani a zaben gwamnan jihar Ondo
A yayin da zaben gwamnan jihar Ondo ke ci gaba da gabatowa, ana ci gaba da nazari kan manyan masu ruwa da tsaki da kuma 'yan siyasa da za su yi tasiri kan makomar sakamakon zaben.
Tun kafin Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta kayyade 10 ga Oktoba na 2020 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben, 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban na ci gaba da fadi tashi.
Tun bayan da INEC ta fitar da jadawalin zaɓen, jam’iyyun siyasa suka fara shirin aiwatar da zaben fidda gwani cikin aminci domin tabbatar da cewa sun tsayar da 'yan takara managarta.
Babu shakka, an sanya idanu kan manyan jam’iyyun siyasa biyu wato APC da kuma PDP, inda ake sa ran wataƙila ɗaya daga cikin jam’iyyun ne za su samar da gwamnan jihar na gaba.
Yayin da zaɓen gwamnan ke kara matsowa, akwai manyan mutane da ke da babban tasiri kan sakamakon zaɓen.
Wasu daga cikin masu tasiri kan zaɓen sun kasance 'yan siyasa yayin da wasunsu ba su da wata alaka da sha'anin siyasa kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.
A yayin da 'ya siyasar sun kasance sanannu, manyan mutanen da ba su da alaka da sha'anin siyasa sun kasance sarakunan gargajiya masu martaba ta farko.
KARANTA KUMA: Matsalar tsaro ta fi ta annobar korona tashin hankali a Kaduna - Annger ya gargadi El-Rufa'i
Daga cikin masu rawanin da ake mutuntawa sun hadar da; Oba Frederick Akinruntan; Oba Victor Kiladejo; Oba Aladelusi Aladetoyinbo; Oba Ajibade Ogunoye; Oba Akadiri Momoh da sauransu.
Ana da yakinin cewa, wadannan sarakuna masu daraja su na da tasiri sosai a duk lokacin zaɓe, musamman na gwamna, inda 'yan takara ke kai musu ziyara har fada domin neman tabarraki.
Misali, Olowo na masarautar Owo, Oba Ogunoye, ya na da 'yan takara kusan goma dake karkashin masarautar sa, wadanda suka hadar har da gwamnan jihar mai ci, Mista Rotimi Akeredolu.
Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar 20 ga watan Yuli ne jam'iyya mai ci ta APC za ta gudanar da zaɓen fidda gwani, inda za ta tsayar da dan takarar da zai rike mata tuta a zaben 10 ga watan Oktoba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng