Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Fom Ga Duk Wanda Ke Son Mallakar Gida a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Fom Ga Duk Wanda Ke Son Mallakar Gida a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da tsarin da zai saukakawa kowane dan Najeriya mallakar gidajen zama cikin sauki
  • A yau Talata, 21 ga watan Mayu ministan gidaje, Ahmed Dangiwa ya kaddamar da shirin a birnin tarayya na Abuja
  • Har ila yau ministan ya bayyana matakan da kowane dan kasa zai bi kafin shiga cikin shirin da cin moriyarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gwamantin tarayya ta kaddamar da shafin yanar gizo da zai ba yan Najeriya damar mallakar gidajen zama cikin sauki.

TINUBU
Gwamnatin Tinubu ta fitar da fom din mallakar gidaje domin saukakawa yan kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna gwamnatin za ta gudanar da aikin ne a karkashin ma'aikatar samar da gidaje ta kasa.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Bayanan da gwamnatin ta fitar sun nuna cewa dukkan yan kasa, waɗanda suke Najeriya da waje za su ci moriyar shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyar shiga tsarin mallakar gidaje

A bayanan da ministan gidaje, Ahmed Dangiwa ya yi yayin kaddamar da shirin, ya nuna cewa za cika fom din shiga tsarin ne ta yanar gizo.

Ministan ya kuma kara da cewa sun samar da tsarin ne cikin sauki ta yadda kowane dan kasa zai iya amfani da shi.

Kyauta gwamnati za ta raba gidajen?

Har ila yau ministan ya bayyana cewa gwamnatin za ta saukaka wa yan kasa hanyar mallakar gidajen ne ba kyauta za ta raba su ba.

Saboda haka ne ma ya ce sun fitar da tsarin da zai ba mutum damar biyan kudin gida nan take da kuma tsarin biya biyu.

Kara karanta wannan

Mata sun shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun kashe mazajensu a Neja

Ya mutum zai shiga tsarin samun gidajen?

Ministan ya bayyana cewa akwai bukatar yin rijista ta yanar gizo da tantance duk mai son cin moriyar shirin.

Bayan haka ya ce za a ba mutane damar zabin gidajen da suka shiga ransu kafin maganar biyan kudi.

A yau Talata ne ministan ya kaddamar da shirin a Abuja, bayan ya yi bayani a kan yadda tsarin zai gudana a kwanakin baya kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

An janye harajin tsaron yanar gizo

A wani rahoton, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya janye umarnin da ya ba bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi na karbar harajin tsaron yanar gizo

Wannan harajin dai na tsaron yanar gizo ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya yayin da wasu ke sukar bankin da ma gwamnatin kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng