Tinubu Ya Nada ’Yar Takarar Sanata a Abuja, Adedayo Sakatariyar Hukumar FCTA

Tinubu Ya Nada ’Yar Takarar Sanata a Abuja, Adedayo Sakatariyar Hukumar FCTA

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada ‘yar takarar sanata a birinin Abuja, Adedayo Benjamins-Laniya mukami a hukumar FCTA
  • Adedayo ta samu mukamin sakatariyar harkokin mata a hukumar a yau Litinin 16 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa
  • Adedayo a matsayin sakatariya za ta yi aiki karkashin Nyesom Wike a matsayin ministan birnin Tarayya Abuja

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Benjamins-Laniyi sakatariyar harkokin mata a hukumar Gudanarwa a Abuja (FCTA).

Hukumar ta FCTA ita ta bayyana nadin Adedayo a cikin wata sanarwa a yau Litinin 16 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.

Tinbub ya nada Adedayo sakatariya a hukumar FCTA
Tinubu Ya Adedayo Sakatariya a Hukumar FCTA. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Waye Tinubu ya nada mukamin sakatariyar FCTA?

Har ila yau, Adedayo ta yi takarar sanata a jam’iyyar APC a mazabar birnin Abuja a zaben da aka gudanar a wannan shekara ta 2023.

Kara karanta wannan

‘Nadin Shugabannin EFCC, ICPC Daga Yanki Daya Ba Adalci’, Lauya Falana Ya Soki Tinubu, Ya Ba Shi Shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar nadin, an yada ta ne a shafin hukumar FCTA na Twitter kamar haka:

“Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Adedayo Benjamins-Laniyi a matsayin sakatariyar harkokin mata a hukumar FCTA.”

Waye gargadi Falana ya yi wa Tinubu kan nadin shugabannin EFCC, ICPC?

Kun ji cewa sharararren lauya, Femi Falana ya soki tsarin yadda Tinubu ya nada shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede inda ya ce ya sabawa doka.

Falana ya ce rashin adalci ne nada shugabannin hukumomin EFCC da ICPC daga yanki daya na kasar.

Ya ce kamata ya yi daya ya fito daga yankin Arewa daya kuma daga yankin Kudancin Najeriya.

inda ya ce idan akwai gurbin mukami guda biyu za a raba su dai dai tsakanin yankin Kudu da Arewa ba tare da fifita daya ba.

Kara karanta wannan

Ma’aikata ba Su Kaunar Shugabar da Tinubu Ya Nada, Sun Hana ta Shiga Ofis

Ya kara da cewa idan kuma akwai gurbin mutane shida to ko wane yanki zai samu mukamin mutum daya a fadin kasar.

Tinubu ya nada Imam a matsayin shugaban FERMA

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ta nada Injiniya Imam Ibrahim Imam a matsayin shugaban kula da gyaran hanyoyi ka Gwamnatin Tarayya (FERMA).

Imam ɗa ne ga dan takarar gwamna a jihar Borno a jam'iyyar PDP kuma jigon jam'iyyar.

Imam matashi ne dan shekara 24 wanda ya kammala karatunsa a Jami'ar Brighton da ke Ingila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel