Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Game da Matashin da Tinubu Ya Nada Shugaban FERMA

Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Game da Matashin da Tinubu Ya Nada Shugaban FERMA

FCT, Abuja – Nadin dan shekaru 24 a matsayin shugaban hukumar FERMA ya samu karbuwa bayan mutane sun yabi nadin ganin yadda matasa ke samun mukamai a wannan gwamnati.

Shugaba Bola Tinubu ya nada mambobin hukumar FERMA 14 wanda dan jihar Born Injiniya Imam Ibrahim Kashim ke jagoranta.

Abubuwa 4 da ba ku sani ba game da matsashin da Tinubu ya nada shugaban FERMA
Tinubu Ya Nada Matashi Imam Kashim a Matsayin Shugaban FERMA. Hoto: Bola Tinubu, Imam Mohammed.
Asali: Twitter

Injiniya Imam shi ne mafi karancin shekaru a cikin jerin dukkan wadanda Tinubu ya nada tun bayan hawanshi karagar mulki.

Legit ta jero muku abubuwan da ya kamata ku sani kan sabon shugaban hukumar FERMA:

1. Shekaru

An haifi Injiniya Imam Ibrahim Kashim a watan Disamba ta shekarar 1998 wanda a yanzu ya na da shekaru 24 da watanni 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Imam shi ne mafi karancin shekaru a cikin dukkan nade-naden da Shugaba Tinubu ya yi a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Manya-Manyan Malaman Musulunci 5 da Su Ka Halarci Walimar Auren Gata a Kano

2. Karatu

Injiniya Imam ya kammala digiri dinsa a Jami’ar Brighton da ke Ingila inda ya karanta bangaren injiniya da ake kira ‘Mechanical Engineering’.

Imam ya samu sakamako ajin farko (First Class), ya kuma yi karatun digiri dinsa na biyu a Jami’ar ta Brighton inda ya yi bautar kasa a watan Agusta na shekarar 2022.

3. Mukami

Kafin samun mukamin da Bola Tinubu ya nada shi, Imam Kashim ya kasance hadimin ministan Ayyuka kuma tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, The Nation ta tattaro.

4. Mahaifi

Imam ya kasance ‘da ga jigon jam’iyyar PDP, Kashim Ibrahim Imam wanda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar a jihar Borno.

Kashin ya yi takarar gwamnan ne a shekarun 2003 da 2007 a jihar inda jam’iyyar ANPP ta mishi cin kaca da mummunar a kaye.

Yaushe Tinubu ya nada Imam?

A jiya shugaba Tinubu ya nada Imam Kashim Ibrahim a matsayin shugaban hukumar FERMA da wasu mambobi guda 14 da za su yi tsawon wa’adi na shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar FERMA da Wasu 11, Ya Naɗa Sabbi

Shugaban ya musu fatan alkairi tare da kwabansu da su yi aiki tukuru don ganin an samu abin da ake nema.

Tinubu ya yi sabbin nade-nade a hukumar FERMA

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Tarayya, FERMA.

Tinubu ya nada Injiniya Imam Ibrahim Kashim a matsayin shugaban hukumar bayan nada mambobi a guda 14 a hukumar.

Hadimin shugaba a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a jiya Juma’a 13 ga watan Oktoba a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.