'Yar TikTok Ta Sauke Jiji da Kai, Ta Nuna Sana’ar da Mahaifiyarta Ke Yi, Tana Taya Ta Aiki

'Yar TikTok Ta Sauke Jiji da Kai, Ta Nuna Sana’ar da Mahaifiyarta Ke Yi, Tana Taya Ta Aiki

  • Wata budurwa mai suna Brown Sugar a TikTok ta sha tofin albarka yayin da aka ga tana taya mahaififyarsa soya garin rogo
  • A wani bidiyon da ta yada mai daukar hankali ta bayyana cewa, babu abin da zai hana ta taimakawa mahaifiyarta duk da iya kwalisanta
  • Wasu 'yan TikTok da dama sun yi martani, sun ce yana da matukar kyau ace matasa na taimakawa iyayensu kafin su zo intanet suna kaudi

'Yan TikTok sun yiwa wata 'yar Najeriya mai kaudi a intanet tofin albarka saboda yadda take taimakawa mahaifiyarta.

A wani bidiyo da ta yada a asusunta na TikTok mai suna @brownsugarnice, ta shawarci 'yan mata masu kwalisa su ke taimakawa iyayensu.

Yadda wata 'yar TikTok ke taya mahaifiyarta soya garin rogo
'Yar TikTok ta sauke jiji da kai, ta nuna sana'ar da mahaifiyarta ke yi, tana taya ta aiki | Hoto: TikTok.@brownsugarnice
Asali: UGC

Kasancewarta 'Slay Queen', hakan bai hana ta ayyukan gida, kuma takan yi amfani da lokacinta yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Dole Ka Tattara Komatsanka Ka Koma Najeriya: 'Yar Amurka Da Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta, Bidiyon Ya Yadu

Ta kuma yada wani hoto na lokacin da ta kammala ayyukanta, sannan ta fita waje domin shakatawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani sashe na biyu na hoton, an ganta a tsaye a wani gidan cin abinci, inda ta shakatawa bayan gama aikinta.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

@Abdul Malik Ikhelowa yace:

"Irin wannan yarinyar ya kamata mutum ya samo, ba irin wadancan marasa ji da suka cika titi ba."

@fatelineogbekhilu yace:

"Allah ya miki albarka yadda kika taimakawa iyayenki sannan kuma kina ci gaba da kwalisarki. Idan da wasu 'yan matan ne boyewa za su yi ba za su nuna ba, Allah zai fallasa su."

@obenejoy yace:

"'Yar uwa, wannan ya taba faruwa dani. Babu abin da zai durkusar da mu 'yan mata."

@Nestafavy29Small ya ce:

"Wannan ya faru dani, Allah ya mana albarka."

Kara karanta wannan

Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40

@Queen joy tace:

"Nima na taba yin wannan amma matsalar wasu mutanen suna ganinka ba ma za su yi maka magana ba, amma gashi yanzu suna ta ihu, irinsu ne."

@fabulousqueen00 Rosemary tace:

"Ina kaunar yin wannan sosai."

Yadda Budurwa Ta Hada Shagalin Murnar Haihuwarta, Amma Kawayenta Suka Yi Zuwa

A wani labarin, wata matashiya mai shekaru 18 ta zaman zugum yayin da ta yi bikin cika shekara amma babu wanda ya hallara.

Mutane da dama sun nuna kauna da taya ta shagalai ganin yadda aka kowa ya guji zuwa wurin wannan shagali.

Wata mata da tace 'yar uwar budurwa mai shagalin ne ta yada bidiyo a TikTok, ta nuna yadda dakin shagalin ya kasance babu kowa a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel