Jami'an Tsaro Sun Halaka Yan Bindiga 67, Sun Ceto Mutane 20 a Jihar Bauchi

Jami'an Tsaro Sun Halaka Yan Bindiga 67, Sun Ceto Mutane 20 a Jihar Bauchi

  • Jami'an tsaron haɗin guiwa sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 67, sun ceto mutane sama da 20 da aka yi garkuwa da su a Bauchi
  • Gwamna Bala Muhammed ya jinjina wa jami'an tsaron bisa wannan nasara kana ya umarci su kawar da 'yan bindiga baki ɗaya
  • Ya ce idan babu zaman lafiya da tsaro, ci gaba ba zai taɓa samuwa ba, yana mai cewa matsalar tsaro ta zama abin damuwa a Bauchi

Bauchi - Jami’an tsaro da suka ƙunshi ‘yan sanda, sojoji, mafarauta da ‘yan banga sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga 67 a karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.

Rahoton Daily Trust ya ce rundunar ta kuma ceto mutane fiye da 20 da aka yi garkuwa da su tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda 8 da alburusai da dama a yankin Lere.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da tawagarsa.
Jami'an Tsaro Sun Halaka Yan Bindiga 67, Sun Ceto Mutane 20 a Jihar Bauchi Hoto: @SenBalamohammed
Asali: Twitter

Sarkin Lere, Malam Jamilu Aliyu Bawa, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin da yake bayani ga Gwamna Bala Mohammed, wanda ya je yankin domin gane wa idonsa.

Basaraken ya shaida wa mai girma gwamnan cewa dakarun sun yi wannan namijin aiki ne bisa umarnin kwamishinan hukumar ‘yan sandan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa ‘yan banga da mafarauta a yankin sun shirya tsaf domin ganin an fatattaki ‘yan bindigar gaba daya da kuma ceto sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

Ƙauran Bauchi ya jinjina wa jami'an tsaro

A nasa jawabin, Ƙauran Bauchi ya ce babu wurin ɓuya ga masu aikata muggan laifuka a jihar, ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa nasarar da suka samu.

Ya umarce su da su farauto ‘yan bindiga dun inda suka ɓuya tare da ci gaba da kawar da su daga doron duniya da nufin dawo da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya da samar musu da kayan aiki a yaƙin da suke da rashin tsaro a fadin jihar.

Mohammed ya ja kunnen jami’an tsaro da su yi taka-tsan-tsan game da wadanda ke shigowa daga jihohin Arewa maso Yamma ta hanyar tabbatar da bayanan da suka dace don raba na gari da mugu.

Ya kara da cewa idan babu tsaro da zaman lafiya, babu wani ci gaba da zai samu. A cewarsa matsalar tsaron jihar Bauchi na ƙara zama abin damuwa, Leadership ta tattaro.

"Muna Tare da Palastine" 'Yan Shiga Sun Fito Tattakin Goyon Baya a Abuja

A wani rahoton kuma Wasu gungun mabiya aƙidar shi'a a Najeriya sun fito tattakin nuna goyon baya ga Falasɗinawa bayan sabon yaƙin da ya ɓarke.

Sheikh Sidi Munir Sokoto, ya ce ƙungiyar Shi'a IMN karkashin Sheikh Zakzaky ra saba gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama tsagerun 'yan bindiga a Zaria bayan sacewa da kashe mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel