NNPC Ya Yabawa Tinubu Kan Cire Tallafin Mai, Ya Ce Saura Kadan Kamfanin Ya Durkushe

NNPC Ya Yabawa Tinubu Kan Cire Tallafin Mai, Ya Ce Saura Kadan Kamfanin Ya Durkushe

  • Mele Kyari, shugaban NNPC ya ce matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na cire tallafi abin a yaba ne
  • Ya ce matakin ne ya ceto kamfanin mai na NNPC daga durkushewa saboda tsananin rashin kudade
  • Kyari ya yi wannan karin haske ne a jiya Litinin 9 ga watan Oktoba yayin wani taro da kungiyar PENGASSAN a Abuja

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa biyan kudin tallafi ya kusa durkusar da kamfanin.

Ya ce a halin da ake ciki Najeriya za ta fara fitar da man fetur zuwa shekarar 2024 don wadata kasar.

'Tinubu ya ceto kamfanin NNPC daga durkushewa, Kyari
NNPC Ya Yabawa Tinubu Kan Cire Tallafin Mai. Hoto: NNPC.
Asali: Twitter

Meye NNPC ya ce kan matatun mai a kasar?

Kyari ya bayyana haka ne yayin taron kungiyar PENGASSAN a Abuja a jiya Litinin 9 ga watan Oktoba, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPC Ya Fadi Abubuwa 2 da Su ka Jawo Layin Mai a Garuruwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyari ya ce kammala matatar mai a kasar zai samar da makamashi kuma zai inganta kasuwancin masana'antun mai a kasar.

Ya kara da cewa matatun mai din za su fara aiki ne kafin karshen shekara wanda zai samar da wadataccen mai a kasar don amfanin yau da kullum.

Wane sako NNPC ya tura ga Tinubu kan cire tallafi?

Ya ce:

"Tun daga 2022 har zuwa 29 ga watan Mayu ko kwabo daya ba a biya NNPC ba na kudin tallafi.
"Wannan shi ya ke tabbatar da cewa mu muke biyan kudaden bayan tattara su daga haraji da sauran hanyoyi.
"Abin nufi anan shi ne da an ci gaba da haka da NNPC zai iya durkushewa saboda matsalar kudi na biyan tallafi.

Kyari ya kara da cewa matakin da Bola Tinubu ya dauka na cire tallafi shi ya kare NNPC daga durkushewa, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC Ya Yi Martani Kan Ba Da Kwangiloli Ga Wasu Shafaffu Da Mai A Arewa Cikin Sirri, Ya Fayyace Komai

Ya ce tabbas matakin abin a yaba ne kuma zai rage yawan cin hanci saboda duk inda ake samun kudaden tallafi dole akwai ci hanci ta hanyoyi da dama.

NNPC ya karyata ba da kwangiloli a boye

A wani labarin, shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya musanta cewa sun ba da kwangilolin gyara bututun mai a boye.

Kyari ya ce kamfanin ya bi duk hanyar da ta dace na ba da kwangilolin kamar yadda doka ta tsara tare da tallata su ga masu bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel