Tinubu Zai Dawo Da Shirin ‘Tradermoni’ Don Tallafawa Kananan ’Yan Kasuwa Da Kawar Da Talauci

Tinubu Zai Dawo Da Shirin ‘Tradermoni’ Don Tallafawa Kananan ’Yan Kasuwa Da Kawar Da Talauci

  • Shugaba Tinubu ya dawo da shirin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari don rage radadin talauci a kasa
  • Tinubu ya dawo da shirin ne na ‘Tradermoni’ wanda ake bai wa kananan ‘yan kasuwa rance don tallafawa kasuwancinsu
  • Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ta ce a wannan karo Naira dubu 50 masu cin gajiyar za su samu na lamuni

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta dawo da shirin ‘Tradermoni’ na tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Nuwamba.

Wannan karo masu cin gajiyar shirin za su samu Naira dubu 50 don taimakawa harkokin kasuwancinsu madadin dubu 10 da a baya ake ba su.

Tinubu zai dawo da shirin 'Tradermoni' don rage talauci
Tinubu Zai Dawo da Shirin ‘Tradermoni’ A Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, Betta Edu.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ce kan shirin 'Tradermoni'?

Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ita ta bayyana haka a gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 8 ga watan Oktoba a Abuja.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta tattaro cewa an kaddamar da shirin ‘Tradermoni’ ne a shekarar 2018 don rage radadin talauci a tsakanin al’umma.

Yayin sanar da dawo da shirin, Edu ta ce:

“A yanzu karon farko, a watan Nuwamba za mu zabi babbar kasuwa a mazabu uku da mu ke da su a ko wace jihar don ba da tallafin ga ‘yan kasuwa.”

Wane tsari Tinubu ya dauko na shirin?

Edu ta ce wadanda za su ci gajiyar shirin za a zabe su ne ba tare da bambanci na jam’iyya ko kuma wani alfarma ba a cikin al’umma.

Ta ce bayan an zabi masu cin gajiyar, za a bude musu asusun banki wanda za su samu kudadensu ta ciki daga Babban Bankin Najeriya, CBN.

Har ila yau, Edu ta ce wadannan kudade da za a bayar babu kudin ruwa a ciki kuma duk wadanda su ka biya za su samu damar karin wasu kudaden a gaba.

Kara karanta wannan

Ahaf: Bayan kashe N-Power, Tinubu ya fadi yadda zai sharewa matasa hawaye a Najeriya

Ta tabbatar da cewa wannan shiri ba shi da alaka da siyasa kuma an kirkiri shirin ne don tallafawa mutane kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu a kan haka.

Tinubu ya dakatar da shirin N-Power

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya dakatar da shirin N-Power har sai baba-ta gani saboda wasu matsaloli.

Ministar jin kai da walwala Dakta Betta Edu ta bayyana cewa akwai tarun matsaloli wanda sai an yi kwakkwaran bincike a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel