Ba za mu biya N60,000 ga masu cin moriyar N-Power ba - Gwamnatin Tarayya

Ba za mu biya N60,000 ga masu cin moriyar N-Power ba - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi karin haske game da biyan Naira dubu sittin ga masu cin moriyar shirin N-Power da ake daf da sallama.

Gwamnatin tarayyar ta ce ba za ta biya N60,000 ba a matsayin kudin sallama ga matasan da suka ci moriyar shirin N-Power kamar yadda suka bukata ba.

A ranar Juma'a ne wasu daga cikin matasan da suka ci moriyar shirin N-Power suka gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin tarayya da ke birnin Abuja.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito, matasan sun nemi gwamnatin da ta biya su kudin sallama na naira dubu sittin tare da mayar da su ma'aikata na dindindin.

Matasan sun kuma ja hankalin gwamnatin a kan ministan kula da agaji, bala'o'i da ci gaban al'umma, Sadiya Umar Farouq, da ta sauka daga mukaminta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Rhoda Shaku iliya ta fitar, ta ce gwamnatin za ta kashe biliyoyin nairori wajen wajen ci gaba da wanzuwar shirin yayin da nan gaba za ta sake daukan wani sabon rukuni na matasa.

Ministar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma; Sadiya Umar Farouq
Hoto daga jaridar Vanguard
Ministar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma; Sadiya Umar Farouq Hoto daga jaridar Vanguard
Asali: UGC

Rhoda ta ce bukatar matasan ba ta cikin tsarin shirin na N-Power da aka kaddamar tun fil a zal, kuma babu wani tanadi da gwamnatin ta yi na sallamar matasan domin daukan wani rukunin na daban.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin ba za ta bayar da kyautar kudin da matasan suka bukata ba wanda sun sun tasarma naira biliyan dari 300.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ma'aikatar ta sanar da cewa, akwai masu cin moriyar shirin N-Power 14,020 masu karbar albashi a wasu ma'aikatu na gwamnati daban-daban.

KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun tarwatsa taron ‘yan Shi’a a garin Zaria

Shirin N-Power wanda aka kirkiro tun a shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta samar da shi domin daukar matasa marasa aiki da suka kammala karatu, kuma aka sanya musu alawus na N30,000 duk wata.

Cikin wata sanarwa ta ranar Alhamis da Rhoda Iliya ta fitar, ta ce ba za a biya wasu masu amfanar shirin N-Power alawus ba saboda an gano suna karbar albashi a wasu ma'aikatun na gwamnati.

Ta ce ofishin Akanta Janar na kasa na kokarin ganin an warware matsalar biyan bashin alawus din watannin baya ga masu cin moriyar shirin na N-Power da suka cancanta.

Don haka Ministar Ma'aikatar, ta ke ba da hakuri a kan jinkirin da tantance masu cin moriyar shirin N-Power na hakika ya haddasa.

Ta ce babu shakka da zarar ofishin Akanta Janar na kasa ya kammala warware matsalar, za a saki alawus din ga wadanda suka cancanta.

A baya bayan nan ne ma'aikatar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma, ta bayyana cewa za'a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 a watan Yuni, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel