Wata ’Yar Najeriya Ta Soki Rage Farashin Siminti Da BUA Ya Yi Bayan Ta Tara Kaya A Shagonta

Wata ’Yar Najeriya Ta Soki Rage Farashin Siminti Da BUA Ya Yi Bayan Ta Tara Kaya A Shagonta

  • Wata mata dilar siminti ta koka bayan kamfanin BUA ya rage farashin siminti yayin da ta ke da tulin kaya a shagonta
  • Matar ta yi mamakin yadda kamfanin bai kula da diloli kamar ita ba masu tarin kaya a shago kafin rage farashin
  • Mutane da dama sun yi martani kan faifan bidiyon da aka yadan inda su ke cewa da kara kudin aka yi ba za ta ce haka ba

Wata mata da ke siyar da siminti ta koka kan yadda kamfanin BUA ya rage farashin siminti ba tare da duba yanayinsu ba.

A makon da ya gabata ne kamfanin na BUA ya sanar rage farashin buhun siminti zuwa Naira 3,500, Legit ta tattaro.

Mata ta koka kan yadda BUA ya rage kudin siminti, ta ce ta yi asara
Wata ’Yar Najeriya Ta Soki BUA Kan Rage Farashin Siminti. Hoto: @jid_olams.
Asali: TikTok

Meye matar ke cewa kan farashin siminti na BUA?

Matar ta ce tun bayan rage farashin ba ta siyar da buhun siminti ko guda daya ba da ta ke da su a shagonta.

Kara karanta wannan

Jami'an 'Yan Sanda Sun Fayyace Komai Bayan Kama Wata Mata Da Tulin Harsasai A Jihar Arewa, Sun Fadi Dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar wacce ta fashe da kuka yayin da ta ke kallon tarun buhunan siminti tsoffin saye inda ta ke mamakin meye za ta yi da su tun da babu wanda ya zo siya.

Ta ce wasu na zuwa don mata tayin wulakanci kan Naira dubu 2,000 inda cikin bacin rai ta ke ce musu su kawo dubu daya.

Ta roki gwamnati da kuma kamfanin da su sake duba farashin inda ta ce hakan ya shafi harkar kasuwancinsu.

Wani mai suna @jid_olams ya wallafa faifan bidiyon inda matar ke sheka kuka ganin irin asarar da za ta tafka.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Legit ta tattaro martanin mutane kan wannan bidiyo na matar:

Sir_Shizzy:

“Lokacin da su ka ce sun kara ban ji kina korafi ba, nagane matsalarki.”

iykefelix170:

“Ki mana shiru, idan aka kara kudin zuwa dubu 9, za ta zo nan ta na mana korafi? wannan ke ya shafa.”

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Rage Farashin Siminti Da BUA Ya Yi, Ya Bai Wa Masu Abinci Shawara

Oba67:

“Abin takaici, lokacin da aka kara farashin simintin an sanar da ke ne.”

Olaniyi:

“Amma kullum mu na fatan samun tattalin arziki mai kyau.”

Dada Dele:

“Madam ki rage farashin za su rage miki asara a kamfani.”

Kamfanin BUA ya rage farashin siminti a Najeriya

A wani labarin, Kamfanin BUA ya rage farashin siminti a fadin Najeriya zuwa Naira dubu 3,500 kacal.

Kamfanin ya sanar da cewa wannan doka za ta fara aiki ne a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel