Shugaba Tinubu Ya Amince a Kafa Kasar Biyafara? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaba Tinubu Ya Amince a Kafa Kasar Biyafara? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rubuce-rubuce da aka yi a shafukan sada zumunta, sun yi iƙirarin cewa Najeriya ta buƙaci yankin Kudu maso Gabas da ya fice ya zama ƙasa mai cin gashin kanta
  • Masu rubuce-rubucen sun ce batun Biyafara ya addabi fadar shugaban ƙasa, ta yadda sai da ta yi gaggawar yin magana kan ƴancin Biafra
  • Wani dandali na binciken gaskiya ya binciki iƙirarin tare da bayyana sakamakonsa a cikin wani rahoto da aka buga a ranar Juma'a, 22 ga watan Maris 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Awka, jihar Anambra - Wasu rubuce-rubuce da aka wallafa a dandalin sada zumunta na Facebook, sun yi iƙirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta amince jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya su fice daga ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

Wannan iƙirari ya fito ne a daidai lokacin da wasu ƴan Najeriya na cikin gida da waje, suke ta fafutukar ganin an samar da wata sabuwar ƙasa.

Tinubu bai amince a kafa Biafra ba
Shugaba Tinubu bai amince a samar da kasar Biafra ba Hoto: Sean Gallup, Stefan Heunis
Asali: Getty Images

Wannan sabuwar ƙasar dai an sanya mata sunan ‘Biyafara’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin rubutun na cewa:

"Tinubu ya buƙaci Biafra ta ɓalle domin a samu a zaman lafiya: Batun Biafra ya addabi fadar shugaban ƙasa har ya kai ga yin magana kan ƴancin Biafra."

Rubutun ya haɗa da hoton wani labari ɗauke da tambarin jaridar The Punch, inda suke danganta labarin kan jaridar.

Rubutun da ke jikin hoton na cewa:

"Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan Biafra, ba za mu iya bayar da yankin Kudu maso Kudu ba. Idan jihohi biyar na yankin Kudu maso Gabas na son ɓallewa, za su iya tafiya.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Amma shin wannan iƙirarin gaskiya ne? Wani dandalin binciken gaskiya, Africa Check, ya yi bincike kan batun.

Ɓallewar Biafra: Sakamakon bincike

Bayan binciken da aka yi, dandalin ya bayyana cewa, da a ce hakan gaskiya ne da batun ya zama kanun labarai na gida da waje.

Dandalin binciken ya ce:

"Amma ba mu sami wani rahoto game da shi ba."

Ya yanke hukuncin cewa babu wata shaida da ke nuna gwamnati ta amince jihohin Kudu maso Gabas su ɓalle daga Najeriya.

Kotu ta ki bada belin Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotu ta ƙi yarda da bukatar Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar IPOB, ta neman beli.

Babbat kotun tarayyar wacce ke zamanta a Abuja, a maimakon bada belin Kanu, ta umurci a gaggauta ci gaba da sauraron shari'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel