Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a Aba

Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a Aba

- Wasu mutane a garin Aba, Jihar Abia sun zargi wata mata da satar mazakutar wani mutum

- Sunyi ikirarin cewa ta roki mutumin ya taimaka mata da kudi kwatsam sai ta sace masa mazakuta

- Duk da cewa matar da musanta abinda ake zarginta, sunyi ikirarin ta mayar masa ne bayan anyi barazanar dukan ta

Wani abin tashin hankali ya faru a Aba inda mutane suka taru a suka zagaye wata mata suna zarginta da sace wa wani mutum azakarinsa sannan ta mayar masa.

A wani hoton bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, ana iya ganin matar da alamun kumburi a fuskarta da wuyan ta tamkar an mata duka kamar yadda LIB ya ruwaito.

Mutane sun taru suna zargin ta cewa ta tafi wurin wani mutum ta roki ya taimaka mata da kudi kuma bayan ya bata zai ya ji wani ya girgiza sannan ya nemi mazakutarsa ya rasa a lokacin da ya yi kokarin fitsari.

Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakuta a Aba
Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakuta a Aba. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka

Sun yi ikirarin cewa daga baya ta dawo masa da azakarin bayan an taru an kanta anyi barazanar mata duka.

Sai dai matar kamar yadda bidiyon ya nuna ta ce ba ta sace masa mazakuta ba balantana ta mayar masa. Tana tambayar ta yaya ta mayar masa idan har ta sace.

Duk da ta musanta hakan, sun cigaba da kasancewa a kan bakansu na cewa ta sace masa mazakuta sannan ta mayar masa.

KU KARANTA: Wilbur: Hotunan karen da ya lashe zaɓen kujerar magajin gari a Amurka

Ana iya ganin mutum da ake ikirarin an sace masa mazakutar sanya da riga mai launin bula tare da mutane suna masa rakiya zai shiga dakin gwajin na likitoci.

Sun yi bayanin cewa za su tafi dakin gwajin ne domin tabbatar da cewa mazakutar mutumin tana aiki yadda ya dace.

A yayin da matar ke musanta satar mazakutar, ana iya jin wata murya daga cikin mutanen da suka taru na barazanar kona ta.

Ga dai bidiyon a kasa:

A wani labarin, kun ji cewa Jami'an Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, za su fara amfani da bindiga don kare kansu daga sharrin wasu masu amfani da tituna a Najeriya.

Akinfolarin Mayowa, shugaban kwamitin FRSC a majalisar wakilai ta kasa ne ya sanar da hakan yayin kare kasafin kudin hukumar na 2021 a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164