Alkalin Kotun Zabe A Plateau Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Cin Zarafinshi A Kafar Sadarwa

Alkalin Kotun Zabe A Plateau Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Cin Zarafinshi A Kafar Sadarwa

  • Jama'a da dama na zargin gamayyar alkalan da su ka yanke hukunci a kotun zabe na 'yan majalisun Tarayya da jihohi a Plateau
  • Wanda ya jagoranci tawagar alkalan, Mai Shari'a Muhammad Tukur ya nuna damuwarsa kan yadda mutane ke musu ba'a kan hukuncin kotun
  • Yayin hukuncin, kotun ta kwace kujerun 'yan majalisu na jam'iyyar PDP da dama tare da bai wa jam'iyyar APC

Jihar Plateau - Mai shari'a, Muhammad Tukur ya bayyana yadda jama'a su ka yi ta masa ba'a a soshiyal midiya kan hukuncin kotu.

Alkalin wanda shi ne shugaban alkalan da su ka yanke hukunci na zaben majalisar jiha da ta Tarayya a jihar, Daily Trust ta tattaro.

Alkali ya bayyana yadda aka ci zarafinshi kan hukuncin kotu a Plateau
Alkalin Tukur Ya Koka Kan Cin Zarafinshi. Hoto: Justice Tukur Muhammad.
Asali: Twitter

Meye alkalan ke cewa kan hukuncin kotun a Plateau?

Gamayyar alkalan karkashin jagorancin Tukur sun yanke hukunci inda su ka bai wa jam'iyyar APC nasara na majalisu a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamnan APC A Jihar Arewa, Ta Bai Wa PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan takarkarin jam'iyyar PDP sun yi fatali da hukuncin inda su ka daukaka kara yayin da jama'a da dama su ka zargi alkalan da son kai.

Yayin da ya ke martani, Tukur ya ce babu daya daga cikinsu da aka bai wa kudi don yin hukuncin son kai.

Ya ce:

"Mu na ganin duk abin da ake fada a kan mu, duk da dan uwana ya yi magana akai, nima ya kamata na ce wani abu.
"Sun kwatanta zaben Kaduna a 2021 da kuma na Plateau a 2023, an yi ta yadawa a kafafen sadarwa don yin ba'a a gare ni.
"Shari'ar daban-daban ce saboda a Kaduna mun yi amfani da dokar zaben 2010 yayin da a Plateau mu ka yi amfani da na 2022."

Wane martani sauran alkalan su ka yi a Plateau?

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Ya ce ko wace shari'a daban ce da 'yar uwarta saboda bambancin dokar zabe a shekarun da ake magana, cewar Trust Radio.

A bangarenta, Mai Shari'a Adetujeye ta nuna damuwarta kan yadda mutane su ke zarginsu da hukuncin da aka yanke.

Ta ce:

"Babu irin cin mutuncin da ba a mana ba, su na cewa wai an siye mu, to wanda ya siye ka yau ai ba zai yarda da kai gobe ba"

Kotu ta kwace kujerar kakakin majalisar Plateau

A wani labarin, kotun zabe a jihar Plateau ta kwace kujerar kakakin majalisar jihar Plateau.

Honarabul Moses Sule ya kasance dan jam'iyyar PDP ce, an kwace kujerar tashi kan zargin tafka magudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.