Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamna Sule Na Nasarawa, Ta Tabbatar Da PDP

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamna Sule Na Nasarawa, Ta Tabbatar Da PDP

  • A jihar Nasarawa ma, kotun sauraran kararrakin zabe ta kori Gwamna Sule Abdullahi na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar
  • Kotun ta kuma tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris
  • Kotun ta yi hukuncin ne a yau Litinin 2 ga watan Oktoba a Lafia babban birnin jihar inda alkalai biyu su ka amince da hukuncin

Jihar Nasarawa - Kotun sauraran kararrakin zaben jihar Nasarawa ta kwace kujerar Gwamna Sule na jam'iyyar APC.

Kitun har ila yau, ta tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

Kotu ta kwace kujerar Gwamna Sule a Nasarawa, ta bai wa PDP
Kotun Zabe Ta Rusa Zaben Gwamna Sule Na Nasarawa. Hoto: Sule Abdullahi, PDP.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke tsakanin APC da PDP a Nasarawa?

Yayin yanke hukuncin a yau Litinin 2 ga watan Oktoba, Alkalai guda biyu sun tabbatar da David wanda ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Ɗan Takarar PDP Da Kotu Ayyana a Matsayin Gwamnan Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da daya daga cikin lauyoyin ya ki amincewa da hukuncin kotun kan zaben, TheCable ta tattaro.

Yayin yanke hukunci a manhajar 'Zoom', Mai Shari'a, Ezekiel Ajayi ya tabbatar da cewa David shi ne halastaccen zababben gwamna a jihar.

Wane umarni kotun ta bai wa INEC kan APC a Nasarawa?

Legit ta tattaro cewa daga cikin alkalan biyu sun amince da hukuncin yayin daya daga cikinsu Ibrahim Mishi ya yi biris da hukuncin.

Sule ya nemi zarcewa a karo na biyu yayin da ya fuskanci adawa mai tsauri daga jam'iyyun adawa a jihar.

Kotun ta umarci Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC ta kwace takardar shaidar zabe daga wurin Sule tare da mika ta ga David Ombugadu.

Wannan na zuwa ne bayan David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya kalubalanci zaben Gwamna Abdullahi Sule na APC.

Kara karanta wannan

Alkalin Kotun Zabe Ya Bayyana Yadda Ake Cin Zarafinshi Kan Hukuncin Kotu, Ya Fadi Gaskiyar Abin Da Ya Faru

Kotun zabe ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a Kano

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kano, ta rusa nasarar Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP a jihar.

Kotun ta kuma tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris.

Gawuna wanda dan jam'iyyar APC ne na kalubalantar zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano kan zargin tafka magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel