Kungiyar CAN Ta Taya Al'ummar Musulmai Murnar Bikin Maulidi

Kungiyar CAN Ta Taya Al'ummar Musulmai Murnar Bikin Maulidi

  • Kungiyar CAN ta taya al'ummar Musulmai murnar zagayowar bikin ranar Maulidi da ake gudanarwa
  • Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a yau Laraba 27 ga watan Satumba
  • Ya bukaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da wannan biki wurin kawo zaman lafiya a kasar

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta taya al'ummar Musulmai murnar zagayowar bikin Maulidi.

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a yau Laraba 27 ga watan Satumba, cewar Channels TV.

CAN ta taya Musulmai murnar bikin Maulidi
CAN Ta Tura Sako Ga Al'ummar Musulmai Kan Bikin Maulidi. Hoto: CAN.
Asali: Facebook

Meye CAN ta ce ga Musulmai kan bikin Maulidi?

Okoh ya ce a madadin Kiristoci gaba daya ya na taya Musulmai murnar Maulidi tare da bukatar hadin kai da zaman lafiya .

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

Ya ce karfin Najeriya ya ta'allaka ne ga bambance-bambancen da ke tsakani inda ya bukaci hadin kai da zaman lafiya a kasar.

Ya ce:

"Yayin da mu ke bikin wannan rana mai muhimmanci, mun san da bambance-bambancen da ke tsakani da ya shafi addini da yare da kuma al'adu wanda shi ne ginshikin kasancewar mu kasa."

Wane sako CAN ta tura ga Musulmai kan bikin na Maulidi?

Ya ce ya kamata a kara kaimi wurin mutunta juna da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin addinai guda biyu, Tribune ta tattaro.

Ya kara da cewa:

"A madadin Kungiyar Kiristocin Najeriya, ina ta ya al'ummar Musulmai murnar yin wannan biki cikin koshin lafiya."

A ko wace ranar 12 ga watan uku na shekarar Musulunci ne ake gudanar da wannan biki don tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Wannan na daga cikin bukukuwan da wasu daga cikin Musulmai su ka dauka da muhimmanci a ko wace shekara.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

Tinubu ya taya al'ummar Musulmi bikin Maulidi

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin al'ummar Musulmi kan bikin zagayowar Maulidi da ake yi a duniya.

Tinubu ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale a cikin wata sanarwa a jiya Talata 26 ga watan Satumba.

Shugaban ya roki mabiya da su yi amfani da wannan biki wurin yi wa kasa addu'a da gwamnatinsa don samun nasarar shawo kan matsalolinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel