Maulud: Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bada Hutun Kwana Daya A Najeriya

Maulud: Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bada Hutun Kwana Daya A Najeriya

  • Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ranar hutun Maulidi na shekarar 1445/2023
  • A wata sanarwa, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu
  • Ministan ya taya Musulmai murnar zuwan Maulidi kana ya buƙaci su yi koyi da kyawawan ɗabi'un Annabi SAW

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu domin bukuwan murnar zagayowar Maulidi na shekarar 1445H.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wasu mabiya addinin Musulunci suna bikin Maulidi ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Ministan cikin gida, Mista Tunji-Ojo.
Maulud: Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bada Hutun Kwana Daya A Najeriya Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

FG ta sanar da ranar hutun ne a wata sanarwa da babban Sakataren ma'aikatar cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade, ya fitar da madadin Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Kara karanta wannan

Maulidi: Sakon Shugaba Tinubu Ga Al'ummar Musulmai Yayin Da Ake Shirin Bikin Maulidi

FG ta taya musulmai murna

A sanarwan, Ministan cikin gida ya taya ɗaukacin al'ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar bukukuwan Maulidi na wannan shekarar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma buƙace su da su zama masu ƙaunar juna, haƙuri, da juriya waɗanda su ne kyawawan ɗalibi'un Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) abin koyi.

Ministan ya bukaci matasa su rungumi aiki tukuru da zaman lafiya da sauran ’yan kasa ba tare da la’akari da Addini, akida, matsayi da kabilanci ba.

A rahoton jaridar Vanguard, sanarwan ta ce:

"Nasihar minista ga ’yan Najeriya, ita ce su yi koyi da ɗabi'un fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW na nuna ƙauna ga juna, hakuri, da juriya da karamci"
"Mai girma Minista, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bukaci ‘yan Nijeriya musamman matasa da su rungumi dabi’ar aiki tukuru da zaman lafiya da kowa ba tare da la’akari da addini, akida, da kabilanci ba.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya, Sun Faɗi Rana

"Haka nan kuma su haɗa hannu da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a kokarinta na gina ƙasa wacce dukkan ‘yan kasa za su yi alfahari da ita."

Majalisa ta miƙa sanarwa ga mataimakin gwamnan kan batun tsige shi

A wani rahoton na daban Majalisar dokoki ta aike a takardar sanarwa ga mataimakin gwamnan jihar Ondo kan yunƙurin tsige shi daga kan muƙaminsa.

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan Mista Lucky Aiyedatiwa, ya roƙi Kotu ta dakatar da shirin da majalisa ke yi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel