Gwamna Namadi Ya Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi a Jihar Jigawa

Gwamna Namadi Ya Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi a Jihar Jigawa

  • Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya ayyana ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal, 1445H a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jiharsa
  • Ya ce gwamnatinsa ta amince da wannan hutun ne domin bada damar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW
  • Shugaban ma'aikatan jihar ya roƙi ɗaukacin Musulmai su yi amfani da lokacin wajen roƙon Allah ya kawo zaman lafiya a ƙasa

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin shugabancin gwamna Umar Namadi (Ɗan Modi) ta ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa gwamnatin Jigawa ta bada hutun kwana ɗaya ne domin bukukuwan murnar zagayowar Maulidi na shekarar 2023.

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa.
Gwamna Namadi Ya Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi a Jihar Jigawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Jami'in hulɗa da jama'a na ofishin shugaban ma'aikatan Jigawa (HoS) ne ya faɗi haka a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Laraba a Dutse.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

Ibrahim ya haƙaito shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Muhammad Dagaceri yana cewa gwamna Umar Namadi na jihar ne ya amince da bada hutun na kwana ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa, shugaban ma'aikatan ya ce:

"Ma rubuta wannan takarda ne domin sanar da cewa gwamnati ta ayyana ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal, 1445H wanda ya zo daidai da 27 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu."
"An ba da wannan hutun ne domin muranar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi)."

Ya ce Dagaceri ya umarci ma’aikata da daukacin al’ummar musulmin jihar Jigawa da su kasance masu hakuri da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba.

Mu yi amfani da wannan damar mu roƙi Allah - HoS

HoS ya kuma yi kira ga mazauna da su yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu’o’in neman kariya daga Allah da kuma shiriya ga shugabanni wajen tafiyar da al’amuran jihar da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Majalisa Tsige Mataimakin Gwamnan APC, Ta Bayyana Dalilanta

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutun Maulidi na shekarar 2023, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Wani malamin makaranta a Birnin Kudu, jihar Jigawa, Aminu Muhammad, ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa tabbas sun samu sanarwa a hukumance kan batun hutun.

Ya ce:

"Eh mun samu labari a hukumance, shugaban makaranta ya tara ɗalibau ya faɗa musu ba bu makaranta, kuma daga sama aka aiko."
"Duk da ni bana Maulidi amma naji daɗi gaskiya saboda an bada hutun ne bisa haihuwar Annabin tsira, Muhammad SAW. Muna farin ciki da kasancewar mu Musulmai masu ƙaunar Annabi fiye da komai."

Hukumar Zabe INEC Ta Sanya Ranakun Zaben Gwamna a Jihohin Edo da Ondo

A wani rahoton na daban Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanya ranakun zaben gwamnonin jihohin Edo da kuma Ondo a shekara mai zuwa 2024

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Wa'adin gwamnan Edo zai ƙare ne ranar 11 ga watan Nuwamba, 2024 yayin da gwamnan Ondo zai sauka 23 ga watan Fabrairu, 2025.

Asali: Legit.ng

Online view pixel