Jigawa: Gwamna Namandi Ya Ba Da Hutun Ranar Litinin Kan Muhimmin Abu 1

Jigawa: Gwamna Namandi Ya Ba Da Hutun Ranar Litinin Kan Muhimmin Abu 1

  • Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ayyana ranar Litinin 28 ga watan Agusta, 2023 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar
  • Namadi ya amince da bada hutun ranar Litinin ne domin murnar cikar jihar Jigawa shekara 32 da kafuwa
  • Ya bukaci ma'aikatan jihar su yi amfani da wannan rana wajen bayar da sadaqa da kuma addu'a a madadin jihar Jigawa

Jigawa state - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ayyana ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023 a matsayin ranar hutu ga ma'aikan jihar baki ɗaya.

Gwamnan ya bada wannan hutu ne domin shagulgulan murna na cikar Jigawa shekaru 32 da kafuwa.

Gwamnan Jigawa, Umar Namadi.
Jigawa: Gwamnan APC Ya Ba Da Hutun Ranar Litinin Kan Muhimmin Abu 1 Hoto: Mallam Garba Al-Hadejawy
Asali: Facebook

Hutun kwana ɗayan da gwamnan ya bayar na ƙunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatan Jigawa, Alhaji Hussaini Ali Kila ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

A sanarwan, Gwamna Namadi ya taya ɗaukacin ma'aikata da sauran al'ummar jihar murnar zagayowar wannan rana ta farin ciki, kamar yadda NTA News ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Namadi ya roƙi alfarma

Gwamnan ya kuma roƙi mutane baki ɗaya da su sanya jihar da Najeriya a addu'o'insu yayin da suke bikin tunawa da wannan rana.

Sanarwan ta ce:

"Gwamna Namadi ya shawarci ma’aikata da daukacin al’ummar jihar da su yi amfani da hutun kwana daya wajen godiya ga Allah madaukakin sarki bisa yanayi mai kyau, da zaman lafiya a Jigawa."
"Haka kuma ya buƙaci su yi wa gwamnati mai ci addu’a don aiwatar da manufofi da shirye-shirye na alheri da ta zo da su."

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa an cire jihar Jigawa daga cikin jihar Kano a ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 1991.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Magana Kan Sabon Rikicin Da Ya Ɓarke a Jam'iyyar APC, Ya Gana da Gwamnan Arewa

Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya kafa jihar Jigawa a lokacin mulkinsa.

Shugaba Tinubu Ya Gana da Minista 1 Kan Muhimmin Batu a Villa

A wani rahoton na daban kuma Bola Ahmed Tinubu da Ministan babban birnin tarayya sun yi ganawar sirri a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake jimamin benen da ya rushe, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel