Basaraken Da Aka Tubewa Rawani a Katsina Ya Yi Martani

Basaraken Da Aka Tubewa Rawani a Katsina Ya Yi Martani

  • Tsohon hakimin Kuraye a ƙaramar hukumar Charanchi ta jihar Katsina ya yi martani kan ritayar da gwamnatin jihar ta yi masa
  • Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu ya bayyana cewa ko kaɗan zargin da ake masa na ɗaura aure ba tare da bincike babu gaskiya a ciki
  • Tuɓaɓɓen basaraken ya bayyana cewa kafin ya ɗaura auren sai da ya bi duk hanyoyin da suka dace wajen wayar da kan ma'auratan

Jihar Katsina - Tuɓaɓɓen hakimin Kuraye da ke ƙaramar hukumar Charanchi a jihar Katsina, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu, ya mayar da martani kan tuɓe masa rawani da masarautar jihar ta yi, cewar rahoton Daily Trust.

Hakimin wanda shi ne Sarkin Kurayen Katsina, an ƙwace sarautarsa ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

Basaraken da gwamnan Katsina ya yi wa ritaya ya yi martani
Basaraken da aka tube rawaninsa a Katsina ya yi martani Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Sai dai, a wata sanarwa da darektan watsa labarai na sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Aliyu Yar’adua ya fitar, ya ce an yi masa ritayar ne bisa shawarar majalisar masarautar Katsina.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Jihar Arewa

Wane irin martani tuɓaɓɓen basaraken ya yi

Da yake mayar da martani game da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Alhaji Ahmadu ya kare kansa daga zargin da ake masa na ɗaura aure ba tare da bincike ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tuɓaɓɓen basaraken ya nuna mamakinsa kan yadda masarautar jihar da gwamnatin jihar suka yi magana biyu kan tuɓe masa rawani.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Cikin da mutuntawa, gwamnati da masarautar kamar suna jefawa juna laifi, duk da cewa takardar koken an rubuta ne ga gwamnatin jiha, wanda ya haifar da komai ba ga majalisar masarautar da na ke ma'aikacinta ba a matsayin hakimi."

Basaraken ya ƙara da cewa, haƙiƙa mutanen biyu da ake magana a kai (ma'auratan) sun tuntube shi domin ya jagoranci aurensu a matsayin wanda zai zama waliyyin ɗaya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Gwangwaje Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m, Da Muhimmin Abu 1

Ya bayyana cewa kamar yadda dokar hana tsangwamar masu ɗauke da ƙanjamau ta tanada, ya kai su ga likitan da ya dace domin ba su shawarwari, sannan ya kai su hukumar ƙaki da cutar ƙanjamau ta jihar (SACA).

Ya ƙara da cewa akwai dukkanin bayanai na likita, da yarjejeniyar da ma'auratan suka ƙulla bayan an ba su shawarwari, wanda hakan ya sanya ɗaura musu auren ba tare da takardar gwajin ba.

Daga ƙarshe ya nemi jama'a da su yi alƙalanci kan wannan laifin da aka ɗora masa.

Gwamnatin Katsina Ta Fara Rabon Tallafi

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Katsina, ta ƙaddamar da fara rabon kayan tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe, shi ne ya ƙaddamar da rabon kayan tallafin a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel