Zamfara: Daliban Jami'ar Gusau Sun Balle da Zanga-Zanga, Sun Toshe Babban Titi

Zamfara: Daliban Jami'ar Gusau Sun Balle da Zanga-Zanga, Sun Toshe Babban Titi

  • Wasu dalibai sun tsunduma zanga-zangar lumana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ranar Asabar, 17 ga watan Yuni, 2023
  • Ɗaliban waɗanda mafi akasarinsu suna karatu ne a jami'ar tarayya da ke Gusau sun fara zanga-zanga ne kan abokan karatunsu ɗalibai 5 da aka sace
  • Rahoto ya nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe babban titin Sakkwato zuwa Zariya wanda ya ratsa ta Gusau

Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka wasu ɗaliban sun tsunduma zanga-zanga a Gusau, babban birnin jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa ɗaliban sun ɓalle da wannan zanga-zanga ne kan abokan karatunsu ɗalibai 5 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Dalibai masu zanga-zanga a Gusau.
Zamfara: Daliban Jami'ar Gusau Sun Balle da Zanga-Zanga, Sun Toshe Babban Titi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mafi akasarin masu zanga-zangar ɗalibai ne a jami'ar tarayya da ke Gusau kuma zuwa yanzu sun toshe babban Titin Sakkwato zuwa Zariya, wanda ya bi ta Gusau.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Fasinjoji Da Dama a Wata Jiha, Rayuka Masu Yawa Sun Salwanta

Rahoton TVC News ya nuna cewa zanga-zangar ɗaliban jami'ar ya haddasa cunkoso a kan babban Titin, masu motocin haya da fasinjoji sun maƙale ba hanyar wucewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindigan jeji da masu garkuwa da mutane.

'Yan bindiga sun kashe kwararren Likita

A ranar Litinin da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka yi ajalin kwararren Likita kuma suka yi awon gaba da mutane 10 ciki harda iyalansa a ƙauyen Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara.

Mazauna garin sun shaida cewa 'yan ta'addan sun shiga garin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Garin Jnagebe na ɗaya daga cikin yankuna da suke fama da hare-hare 'yan fashin daji a kai a kai. Daga watan Janairu, 2023 zuwa yau, mazauna sun ce aƙalla sau huɗu 'yan ta'adda suka kai musu hari.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Gwamna Lawal Ya Fara Ɗaukar Matakan Kawo Karshen Yan Bindiga a Zamfara

Idan baku manta ba, a watan Fabrairu, 2021, mahara suka yi awon gaba da aƙalla ɗalibai mata 200 daga wata Sakandire a cikin garin Jangebe.

Ɗalibin jami'ar 'Federal University Gusau' ya shaida wa Legit.ng Hausa ta wayar tarho cewa tabbas sun yi zanga-zangar ne a garin Damɓa domin nuna fushi da yawan garkuwa da ɗalibai.

A cewarsa, abokan karatunsu na zama a gidajen ɗalibai masu zaman kansu a Damɓa, kuma yan bindiga suna musu ɗauki ɗai-ɗai, su zo su tafi da ɗaya, biyu wani lokacin 5.

Ɗalibin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda hali na tsaro, ya shaida wa wakilinmu cewa:

"Eh tabbas mun yi zanga-zanga duk da ban samu zuwa ba saboda a can Damɓa ne aka yi. Abokan karatunmu na zama a Damɓa, to 'yan bindiga mun matsa mana, su sace 1, 2 wani lokacin 5."
"Babu wani mataki da ake ɗauka shiyasa ɗaliban da ke zama a wurin suka gaji suka fito wannan zanga-zanga. Sai da aka turo motocin sojoji sannan ɗaliban da suka fita suka hakura."

Kara karanta wannan

Gwamna Radɗa Ya Jagoranci Gwamnoni 6 Sun Gana da Tinubu Kan Muhimman Abu 2 da Suka Shafi 'Yan Arewa

Ya kara da cewa ɗalibai sun so ƙara fita zanga-zanga washe gari ranar Lahadi amma Sojoji suka hana su, yanzu haka dai an tura sojoji da yawa Damɓa.

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai

A wani rahoton na daban Yan bindigan da ake zaton masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ne sun yi awon gaba da Malamin Coci a jihar Benuwai.

Malamin Cocin da maharan suka yi garkuwa da shi yana aiki a St. Margaret’s Parish da ke garin Ajegbe Awume, ƙaramar hukumar Ohimini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262