CJN Ariwoola Ya Ba Sabbin Alkalai 9 Na Kotun Daukaka Kara Rantsuwar Kama Aiki

CJN Ariwoola Ya Ba Sabbin Alkalai 9 Na Kotun Daukaka Kara Rantsuwar Kama Aiki

  • Alƙalin alƙalai na Najeriya, mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya rantsar da wasu alƙalai tara na kotun daukaka ƙara
  • Sabbin alkalan sun fito ne daga sassa daban-daban na jihohin ƙasar nan, kuma tun da farko an rantsar da su a matsayin alƙalan babbar kotun
  • Yana da kyau a lura cewa sabbin alƙalan za su kasance cikin alƙalan da za su saurari ɗaukaka ƙara da dama daga sakamakon hukuncin kotunan zaɓe a ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, AbujaMai shari’a Olukayode Ariwoola, alƙalin alƙalan Najeriya, ya rantsar da sabbin alkalai tara na kotun daukaka ƙara da aka naɗa kwanan nan.

Jaridar Independent ta rahoto cewa alƙalan na kotun ɗaukaka ƙarar an rantsar da su ne a ranar Laraba, 20 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Jihar Arewa

Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan kotun daukaka kara
CJN Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan kotun daukaka kara Hoto: Justice Olukayode Ariwoola
Asali: Twitter

Alƙalan da aka rantsar ɗin sun haɗa da Binta Fatima Zubairu daga jihar Kaduna, an nada ta alƙalin babbar kotun tarayya a ranar 31 ga Oktoba, 2001; Peter Chudi Obiora daga jihar Anambra, wanda aka rantsar da shi a matsayin alkalin babbar kotu a ranar 17 ga watan Janairun 2005.

A cewar rahoton Vanguard, akwai mai shari'a Hannatu Azumi Laja-Balogun daga Jihar Kaduna, wacce aka naɗa a matsayin alkalin babbar kotun tarayya a ranar 24 ga Mayun 1999.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin sunayen sabbin alƙalan kotun daukaka ƙara

Sauran Alkalan da aka rantsar da su sun hada da: Asma’u Musa Mainoma daga babban birnin tarayya Abuja, an nada ta alkalin babbar kotun tarayya a ranar 1 ga Fabrairu 2013; Jane Esieanwan Iyang daga jihar Cross River, wacce aka rantsar da ita a matsayin alkalin babbar kotu a ranar 12 ga watan Fabrairun 2015.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Maka Shugaban Kasa Tinubu a Gaban Kotu Kan Wani Muhimmin Abu 1

Lateef Adebayo Ganiyu daga jihar Oyo, wanda ya zama alkalin babbar kotu a ranar 26 ga watan Yuni 2014; da Okon Efreti Abang daga jihar Akwa Ibom, wanda aka nada shi a matsayin alkalin babbar kotu a ranar 22 ga watan Yuni 2009.

Sauran su ne mai shari’a Hadiza Rabi’u Shagari daga Jihar Sakkwato, wacce ta zama alƙalin babbar kotu a ranar 12 ga Fabrairu, 2015; da Paul Ahmed Bassi daga jihar Borno, wanda aka naɗa a matsayin alƙalin babbar kotu a ranar 14 ga Yuli, 2017.

Rantsar da alƙalan na zuwa ne a daidai lokacin da kotuna a faɗin ƙasar nan ke yanke hukunci kan karar da ƴan takarar siyasa a matakai daban-daban suka shigar kan wadanda suka yi nasara a babban zaɓen 2023.

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano, ta tsige gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na jam'iyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel