Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Taraba

Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Taraba

  • Jam'iyyar PDP ta ƙara rasa kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Taraba ɗaya a gaban Kotun sauraron ƙararrakin zabe mai zama a Jalingo
  • Kotun ta kwace nasarar ɗan majalisar ta kuma tabbatar da zaben wasu ƙarin 'yan majalisun jiha biyu na APC
  • Alkalin Kotun, mai shari'a Benson Ogbu ya yanke wannan hukunci ne da daren ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jalingo, jihar Taraba - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zama a Jalingo, babban birnin jihar Taraba ta soke nasarar ɗan majalisar jiha, Nuhu Akila, na jam'iyyar PDP.

Kotun ta yanke hukuncin soke nasarar Akila na jam'iyyar PDP tare da bayyana mai shigar da ƙara kuma ɗan takarar APC, Emmanuel George, a matsayin wanda ya ci zaɓe.

Kotu ta yanke hukunci kan zaben yan majalisar jiha guda uku.
Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Taraba Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Alkalin ya kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta kwace takardar shaidar lashe zaɓen da ta bai wa Akila, kana ta miƙa wa Emmanuel George, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Cikin NNPP Ya Ɗuri Ruwa a Kano, Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Nasarar Abba Gida-Gida

Da yake martani kan wannan hukunci, ɗan takarar APC, George ya nuna farin cikinsa bisa wannan nasara da ya samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Adalci ya yi nasara. A baya mun fadi cewa mu ne muka samu mafi rinjayen kuri’un halal da aka kada a zaɓen," inji shi.

Kotu ta tabbatar da nasarar 'yan majalisu 2 na APC

Haka nan kuma Kotun ta tabbatar da nasarar 'yan majalisu biyu na APC, Batulu Mohammed, mai wakiltar mazaɓar Gashaka da Abel Peter na mazaɓar Mbamnga a majalisar dokokin Taraba.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Benson Ogbu ta kori kararakin da aka shigar gabanta na kalubalantar nasarar 'yan majalisar jihar guda biyu na APC, Guardian ta rahoto.

'Yan takarar jam'iyyar PDP a mazaɓun gudan biyu, Umar Gayam na mazaɓar Gashaka da Emma Bongo na mazaɓar Mbamnga ne suka shigar da ƙararrakin biyu.

Kara karanta wannan

Matawalle vs Dauda: Kotun Zaben Gwamnan Zamfara Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci

Sun gabatar da hujjoji a gaban Kotun cewa 'yan takarar APC da INEC ta ba nasara ba su cancanta ba kuma an saɓa wa dokokin zaɓe, amma kotun ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya.

Kamfanin NNPCL Ya Yi Tankade da Rairaya, Ya Kori Manyan Jami'ai Daga Aiki

A wani rahoton na daban Kamfanin mai na gwamnatin tarayya (NNPCL) ya yi tankaɗe da rairaya a ɓangaren ma'aikata ranar Talata.

A wata sanarwa da ya fitar da safe, kamfanin ya kori manyan ma'aikatan da ya rage musu ƙasa da watanni 15 su yi ritaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262