An Bayyana Albashin Da Shugaba Tinubu Ke Samu a Kowane Wata

An Bayyana Albashin Da Shugaba Tinubu Ke Samu a Kowane Wata

  • Hukumar da ke da alhakin yanke albashin ma'aikata da ƴan siyasa a Najeriya ta bayyana ainihin abin da Shugaba Tinubu ke samu a matsayin albashi
  • Shugaban hukumar ta RMAFC ya bayyana cewa albashin shugaban ƙasar bai kai naira miliyan ɗaya da rabi ba (N1.5m) a kowane wata
  • Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa saɓanin abin da ƴan Najeriya ke hasashe, masu riƙe da muƙaman siyasa ba su da wani albashi mai tsoka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban hukumar RMAFC mai alhakin yanke albashin ma'aikata da ƴan siyasa a Najeriya, Alhaji Muhammed Shehu, ya bayyana albashin da Shugaba Tinubu yake samu a kowane wata.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa albashin shugaban ƙasan bai kai naira miliyan ɗaya da rabi ba (N1.5m).

RMAFC ta bayyana albashin Tinubu
Hukumar RMAFC ta ce albashin Tinubu bai kai N1.5m a wata ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar PM News ta kawo rahoto cewa, Shehu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan 87, An Fadi Abinda Kowane Dan Ƙasa Zai Biya

Ya bayyana cewa minista kuma yana samun ƙasa da miliyan daya kowane wata a matsayin albashinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin ƴan kwanakin nan ƴan Najeriya sun yi Allah-wadai da rahotannin shirin da hukumar ta yi na ƙara wa masu riƙe da muƙaman siyasa kaso 114 na albashi, a daidai lokacin da ake cikin halin matsin tattalin arziki a ƙasa.

Shin ƴan siyasa na samun albashi mai tsoka?

Sai dai Shehu ya dage kan cewa masu rike da mukaman siyasa a Najeriya ba sa samun wani albashi wanda ya wuce ƙimakamar yadda ƴan Najeriya ke hasashe, cewar rahoton Within Nigeria.

Shehu ya bayyana bayanin karin albashin da ba gaskiya ba ne.

Ya tabbatar da kundin tsarin mulki ya ɗora alhaki kan hukumar RMAFC na yanke wa tare da duba kan albashin jami’an zartaswa, ƴan majalisa da na shari’a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya, An Faɗi Sunayensu

A cewar Shehu, lokaci na ƙarshe da aka yi duba kan albashin masu rike da muƙaman siyasa a Najeriya, shi ne a shekarar 2007.

SERAP Ta Maka Tinubu a Kotu

A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ƙara a gaban wata babbar kotu a jihar Legas.

Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne domin neman kotun ta tilasta shugaban ƙasan ya hana tsaffin gwamnoni daga cikin ministocinsa karɓar kuɗin fansho daga aljihun jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng