Cikakkun Sunaye: Manyan Nade-Nade 11 Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi a Kwanaki 15 Na Satumba

Cikakkun Sunaye: Manyan Nade-Nade 11 Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi a Kwanaki 15 Na Satumba

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Zacch Adedeji a matsayin sabon shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS) a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba.

Kafin sabon nadin nasa, Adedeji ya kasance mai ba shugaban kasar shawara ta musamman kan kudaden shiga kuma ya ba da shawarwari da dama kan yadda za a tattara kudaden shiga a kasar.

Nadin Adedeji ya biyo bayan tsige Mohammed Nami, tsohon shugaban hukumar harajin, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada.

Tinubu ya yi wasu nade nade 11 a watan Satumba
Cikakkun Sunaye: Manyan Nade-Nade 11 Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi a Kwanaki 15 Na Satumba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nadin Zacch Adedeji shine irinsa na goma sha daya da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi cikin kwanaki 15 na watan Satumba.

Ga jerin nade-naden da Shugaban kasa Tinubu ya yi a kasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanu Yanzu: Tsohon Shugaban Hukumar FIRS Da Tinubu Ya Tsige Ya Magantu

1. Zacch Adedeji

Shugaban kasa Tinubu ya nada Adedeji a matsayin mukaddashin shugaban hukumar FIRS a ranar Alhamis.

Tsohon kwamishinan kudin na jihar Oyo zai karbi mulki daga hannun Mohammed Nami, wanda ya aka nemi ya tafi hudun ritaya nan take.

2. Aliyu Tijani Ahmed

Shugaban kasa Tinubu ya nada shi a matsayin sabon shugaban hukumar masu neman mafaka, baki da 'yan gudun hijira (NCFRMI).

Ahmed ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Nasarawa kuma kwamishinan jihar sau biyu.

3. Delu Bulus Yakubu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Delu Bulus Yakubu a matsayin shugabar Hukumar Jin Dadin Al'umma ta Kasa (NSIPA).

Nadin nata zai tabbata ne idan majalisar Dattawa ta tantance ta tare da tabbatar da ita.

Manyan sakatarori takwas na babban birnin tarayya

A ranar Talata, 5 ga watan Satumba ne shugaban kasa Tinubu ya amince da nadin manyan sakatarori takwas na babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya, An Faɗi Sunayensu

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya rantsar da sakatarorin a ranar Talata, 12 ga watan Satumba a babban cibiyar taro ta kasa da ke Abuja.

Ga jerin sunayen sakatarorin a kasa:

Bitrus L. Garki - Sakataren gudanarwa na birnin Tarayya

2. Lawan Kolo Geidam - Sakataren Noma da raya karkara

3. Danlami Ihayyo - Sakataren ilimi

4.Adedolapo A. Fasawe - Sakataren lafiya

5. Salman Dako - Sakataren bangaren shari'a

6. Chinedum Elechi - Sakataren tattalin arziki da tsare-tsare

7. Uboku Tom Nyah - Sakataren sufuri

8. Muntari Abdulkadir - Sakataren ci gaban al'umma

Tsohon Shugaban hukumar FIRS da Tinubu ya tsige ya magantu

A wani labarin, mun ji cewa Muhammad Nami, tsohon shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS), ya yi martani a kan sauke shi da aka yi daga kujerarsa.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya tsige Nami a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba sannan ya nada mai ba shi shawara ta musamman kan kudaden shiga, Zacchaeus Adedeji, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar harajin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel