Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai 8 A Gwamnatinsa A Ma’aikatar Birnin Tarayya

Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai 8 A Gwamnatinsa A Ma’aikatar Birnin Tarayya

  • Sa’o’i 24 bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya wuce kasar Indiya, ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa a jiya Talata
  • Shugaban ya yi wadannan sabbin nade-naden ne a ma’aikatar gudanarwa ta Birnin Tarayya (FCTA) inda za su ci gaba da aiki
  • Tinubu ya yi wannan nadin a ranar da ya cika kwanaki 100 a kan karagar mulki tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi manyan nade-nade a gwamnatinsa a jiya Talata 5 ga watan Satumba.

Wadannan sabbin nade-nade an yi su ne a ma’aikatar gudanarwa ta Birnin Tarayya (FCTA), Legit.ng ta tattaro.

Tinubu ya yi sabbin nade-naden mukamai a gwamnati
Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai 8 A Gwamnatinsa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya yi nade-naden?

Fadar shugaban kasar ce ta bayyana haka a jiya Talata 5 ga watan Satumba a shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Jerin Kararrakin Zaben Da Aka Gudanar Tun Shekarar 1999 Da Sakamakon Da Aka Samu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya yi wannan nadin a ranar da ya cika kwanaki 100 a kan karagar mulki tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Wannan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan shugaban ya tafi Indiya don halartar taron G-20 bayan gayyatar Fira Ministan Indiya, Narendra Modi.

Sabbin nade-naden guda takwas sun hada da:

1. Bitrus L. Garki - Sakataren gudanarwa na birnin Tarayya

2. Lawan Kolo Geidam - Sakataren Noma da raya karkara

3. Danlami Ihayyo - Sakataren ilimi

4.Adedolapo A. Fasawe - Sakataren lafiya

5. Salman Dako - Sakataren bangaren shari'a

6. Chinedum Elechi - Sakataren tattalin arziki da tsare-tsare

7. Uboku Tom Nyah - Sakataren sufuri

8. Muntari Abdulkadir - Sakataren ci gaban al'umma

Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu

A yau Laraba 6 ga watan Satumba kotun kararrakin zaben shugaban kasa za ta yanke hukunci na karshe a Abuja.

Kara karanta wannan

Kwana 100: Maryam Shetty da Wurare 5 da Tinubu Ya Canza Shawara Saboda Matsin Lamba

Tun bayan sanar da Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris, ake fama da shari'a a kotu.

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma na jam'iyyar Labour, Peter Obi sun shiga kotu don kalubalantar zaben da aka gudanar.

'Yan adawar sun zargi Bola Tinubu da tafka mummunan magudi da kuma sauran korafe-korafe da su ka shafi takardun karatun Tinubu.

Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Zaben Shugaban Kasa

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta sanar da ranar Laraba 6 ga watan Satumba a matsayin zaman kotun na karshe wanda za ta yanke hukunci.

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma na jam'iyyar Labour, Peter Obi sun shiga kotu don kalubalantar zaben da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel