Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani ango dan Najeriya ya yi tsallen murna bayan ya ga fuskar kyakkyawar amaryarsa a daren farkonsu
  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuno angon yana bude mayafin da aka lullube fuskar amaryar da shi tare da lekata kafin ya kama tsalle-tsalle
  • Bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya inda mutane da dama suka yi martani kan daukar hankalinsa da amaryar ta yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo mai tsuma zuciya ya nuno yanayin da wani ango ya shiga bayan ya bude fuskar amaryarsa a lokacin da aka kawo masa ita dakinsa a matsayin matarsa ta sunnah.

Mutumin ya cika da tsantsar farin ciki yayin da ya leka fuskar amaryar tasa ta cikin mayafin da aka lullube ta da shi, yayin da ita kuma take zaune a kan gado a darensu na farko.

Kara karanta wannan

“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet

Ango ya yi tsallen murna a daren farko
Ango Ya Yi Tsallen Murna Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @mufasatundeednut/Instagram.
Asali: Instagram

Mutane sun yi hasashen auren hadi ne

Yayin da suke martani a sashin sharhi, mutane da dama da suka kalli bidiyon sun hasashen cewa ko dai auren hadi aka yi masu cewa watakila ba shi da masaniya kan yaya kamannin amaryar yake.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, kowa ya san irin kyawu na musamman da amarya kan yi a ranar aurenta wanda shakka babu wannan ne ya dauki hankalinsa tare da nuna zumudinsa a fili.

Martanin jama'a kan zumudin ango a darensu na farko

@omalishan ta yi martani:

"A lokacin da aka yi maka auren hadi sai kuma amaryar ta zama wacce kake so dama."

@ife luv12 ya yi martani:

"Ya samu daidai abun da ya yi oda."

@eajakad ya yi martani:

"Sabuwa fil a leda, babu wanda ya santa mace. Ba yar sharholiya bace."

Kara karanta wannan

Rashin Tarbiyya: Matashi Ya Dannawa Mahaifansa Kwado A Daki Su Na Bacci, Ya Musu Mummunan Sata

@chyddo ta yi martani:

"Lokacin da ka samu daidai da abun da ka yi oda. Dan uwa ya sha maganin karin jini. Babu sanyin kashi daga yanzu."

@governorscousin ya yi martani:

"Sabuwa fil a leda."

@sadeeq_abdoulsamad ya ce:

"Yan uwana Musulmai mu hadu a nan."

Bidiyon matashiya mai tsukakken kugu ya dauka hankali

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya mai siririn jiki da tsukakken kugu ta fito bainar jama'a, inda masu wucewa suka tsaya tare da zuba mata na mujiya.

A wani bidiyo da aka yada a TikTok, matashiyar mai siririn jiki ta bai wa mutanen da suka gan ta mamaki. Sun fito da wayoyinsu domin daukarta bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel