Bidiyon Wata Matashiyar Budurwa Mai Tsukakken Kugu Da Siririn Jiki Ya Dauka Hankali

Bidiyon Wata Matashiyar Budurwa Mai Tsukakken Kugu Da Siririn Jiki Ya Dauka Hankali

  • Bidiyon wata matashiya mai siririn jiki da tsukakken kugu ya bar mutane baki bude tare da tarin tambayoyi a kwanyarsu
  • Mutane sun yi mamakin ko tana iya numfashi ko kuma tana da kayan ciki saboda yadda kugunta yake a tsuke
  • Amma kuma alamu sun nuna babu abun da ke damun budurwar domin dai tana tafiyarta hankali kwance cikin sauri tare da yi wa masu kallonta murmushi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya mai siririn jiki da tsukakken kugu ta fito bainar jama'a, inda masu wucewa suka tsaya tare da zuba mata na mujiya.

A wani bidiyo da aka yada a TikTok, matashiyar mai siririn jiki ta bai wa mutanen da suka gan ta mamaki. Sun fito da wayoyinsu domin daukarta bidiyo.

Wata matashiya mai tsukakken kugu ta dauka hankali
Bidiyon Wata Matashiyar Budurwa Mai Tsukakken Kugu Da Ramammen Jiki Ya Girgiza Intanet Hoto: Twitter/@Gidi_Traffic
Asali: Twitter

Ta sanya bakakken kaya "biri da wando", wanda ke nuna surar jikinta gaba daya da fallasa tsananin siririnta a fili.

Kara karanta wannan

"Mahaifina Ne Ya Jawo Min", Tsohuwa 'Yar Shekara 95 Da Ba Ta Taba Yin Aure Ba Ta Magantu, Bidiyon Ya Yadu

Yayin da take tafiya, tana ta murmusawa bayan ta lura da yadda mutane ke kallonta tare da daukarta da wayoyinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon wata mata mai tsukakken kugu ya yadu

Kugunta da tumbinta a tsuke suke sosai ta yadda wasu masu amfani da Twitter ke tunanin anya tana da kayan ciki kuwa.

Sai dai kuma wasu sun yaba ma matashiyar sannan sun ce tana da tsantsar kyau. Wasu kuma sun yi mamakin yadda ta iya zimma irin wannan sura na jiki. @gidi_traffic ce wallafa bidiyon.

Kalli biodiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon matashiya mai tsukakken kugu

@gregade ta ce:

"Ta yi kama da abun da za ta karkarye."

@Views09 cta yi martani:

"Duk wannan don kawai a burge namiji wanda bai damu ba. Abun akwai rashin hankali."

@iam_doctormayor ya tambaya:

"Ina fatan kodarta na aiki."

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Tsawon Shekaru 10 Tana Aikin Kula Da Yara, An Mallakawa Matashiya Gida a Abuja

@SpiceThaGlowest ta ce:

"Amma dai tana da kyau."

@Mhr_Rhudy ta ce:

"Haka aka halicce ta."

Hotunan shagalin bikin wani mutum da ya auri mata 7 a rana daya sun yadu

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan kasuwa a kasar Uganda mai suna Habib Nsikonnene, ya angwance da tsala-tsalan yan mata har guda bakwai a rana daya.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, biyu daga cikin amaren nasa uwarsu daya ubansu daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel