“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet

“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet

  • Wata mata mai juna biyu ta yadu a soshiyal midiya bayan bidiyonta ya bayyana a dandalin TikTok
  • A cikin bidiyon, wanda ya bai wa mutane da dama mamaki, matar ta nuna yadda ta koma lokacin da take da juna biyu
  • Jama'a sun yi matarni kan bidiyon, inda wasu da dama suka nuna kaduwarsu kan yanayin yadda fuskarta ta koma

Dandalin soshiyal midiya ya dauki dumi bayan wata mata ta shiga shahararriyar gasar nan ta TikTok.

A cikin bidiyon da ya yadu, ta baje kolin yadda rayuwarta ta kasance a lokacin da take dauke da juna biyu da yadda kamanninta ya koma.

Ciki ya sauyawa wata mata kamanni
“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet Hoto: @prechsempire/TikTok.
Asali: TikTok

Sai dai kuma, a cikin wani bidiyo, ta kasance dauke da farin cikin ranta bayan ta haife abun da ke cikinta.

Mai ciki ta ba mutane mamaki da yadda hanci da fuskarta suka koma

Kara karanta wannan

Wani Mutum Da Ya Fara Sana’ar Ayaba Da Kasa Da N100k Ya Gina Gida 3, Yana Shirin Fadin Sirrin

Abun da ya ja hankalin jama'a shine katon hancinta da kuma fuskarta da ta cika ta tumbatsa. wanda suka alakanta hakan da tarin ruwan da cikinta ke samarwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu sun yi ikirarin cewa tana kama da shahararren dan wasan Najeriya, Mista Ibu.

Mutane sun ce yanayin yadda hancinta ya koma a lokacin da take dauke da juna biyu ya tuna masu da yanayin fuskar shahararren mai kasan barkwancin Mista Ibu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon sauyawar wata mai ciki

Bidiyon ya haifar da martani daga jama'a inda wasu da dama suka nuna mamakinsu kan kamannin nata.

@GraciousDebby ta ce:

"Wai menene matsalar ciki da hanci."

@Izah ta yi martani:

"Kin yi kama da Mista Ibu."

@Genipher.klemz ta ce:

"Ya Allah ka san hancina na da girma dama ka tausaya mun sannan ka rage mun maimakon kara shi."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Aka Manta Kayan Aikin Tiyata a Cikin Wata Mata

@Princess V ta ce:

"Na taya ki murna yar'uwa ni da nake da dogon hanci ban ga mijin aure ba."

@Rozev ta yi martani:

"Mista Ibu kai ne nan."

Idan kana son zama da arziki ka zama mai kankamo, Mawaki Akon

A wani labarin, shahararren mawakin nan dan kasar Senegal, Akon, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi kowa kankamo a duniya.

Fitaccen mawakin ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a matsayin bako a wani shiri tare da Logan Paul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel