Dan Najeriya Ya Mayar Da Tsohuwar Mota Ta Zama Sabuwa Dal a Leda, Bidiyon Ya Ja Hankali

Dan Najeriya Ya Mayar Da Tsohuwar Mota Ta Zama Sabuwa Dal a Leda, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wani matashi dan Najeriya ya nuna yadda ya sauya siffar motar Hilux 2007 da ta tsufa tare da lalacewa
  • Matashin dan baiwar ya mayar da tsohuwar motar zuwa wata dalleliya sabuwa fil a leda kuma hakan ya baiwa mutane mamaki
  • Ya bukaci mutane da su daina yanke kauna da tsoffin motocinsu, maimakon haka su dunga nemansa suka yadda zai mayar da tsohuwa yarinya

Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a TikTok bayan ya baje kolin yadda ya sauya siffar wata tsohuwar Hilux ta koma Tiger 2020.

Mutumin dan jihar Enugu wanda ke sana'ar sauya jikin motoci ya wallafa wani bidiyo a TikTok yana mai nuna lalacewar da motar Hilux din wanda aka kera a 2007 tayi.

Tsohuwa da sabuwar mota
Dan Najeriya Ya Mayar Da Tsohuwar Mota Ta Zama Sabuwa Dal a Leda, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@princepeterson421
Asali: UGC

Daga gwangwani ya yi mata fenti kalar shuni sannan ya sauya jiki da cikin motar.

Kara karanta wannan

Kanwar Maza: Bidiyon Tarairayar da ‘Yan Uwan Amarya Maza 7 Suka yi Mata Wurin Aurenta ya Kayatar

Lamarin ya matukar baiwa mutane mamaki inda suka kasa gaskata cewar sabuwar motar ita ce tsohuwar Hilux wanda ya wallafa a baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake alfahari da aikinsa, ya shawarci jama'a da su dunga kawo masa tsoffin motocinsu domin ya yi masu aikin mai da tsohuwa yarinya.

Ya rubuta a kasan bidiyon:

"...Ba cika baki kawai ku kawo tsohuwar motarku sannan ku ga abun da zan iya yi."

Mai sauya motar ya yiwa Legit.ng bayanin cewa Allah ne ya jagorance shi zuwa cikin wannan aikin da yake yi.

"Nagode sosai Legit.ng. Ina matukar godiya ga tallafin da kuka yi mun ta hanyar tallata ni. Zan iya cewa Allah ne kawai ya jagorance ni da yunwa."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

kcee24558 ya ce:

"Maimakon bata kudi wajen chanja shi. Me zai haka ka yi amfani da kudin sannan ka siya sabuwar kira."

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Ya Ce Mutum Bai Isa Ya Kashe Tinubu Ba Kafin Ko Bayan Zaben 2023

Quinzyjoe ya ce:

"Da Najeriya ce zata zama kasa mafi inganci a Afrika da tarin fasaha da baiwa da Allah ya yi masu."

somibaby01 ya ce:

"Duk wadannan masu shakkun...Don baka da fasaha baya nufin mutane da ke waje irinka ne..."

FL️U®️ℹ️SH ta ce:

"Hakan na nufin cewa duk motocin nan da mutane ke siya su ce sabuwa gal duk gyara ne."

Matashi ya kashe miliyan N1.3 wajen kera gidan laka

A wani labarin, wani matashi ya shayar da mutane mamaki a soshiyal midiya bayan ya baje kolin gidan da ya kera da naira miliyan 1.3 kacal.

Ya yi amfani da katakai, laka wajen ginin sannan a karshe ya yi yabe da siminti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel