"Tinubu Zai Cigaba Da Nasara Akan Atiku, Peter Obi": Hamzat Lawal Ya Bayar Da Dalili

"Tinubu Zai Cigaba Da Nasara Akan Atiku, Peter Obi": Hamzat Lawal Ya Bayar Da Dalili

  • An buƙaci Peter Obi na jam'iyyar Labour Party Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su haɗe waje ɗaya kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Shugaban Connected Development (CODE), Hamzat Lawal, shi ne ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da Legit.ng
  • Lawal ya bayyana cewa siyasar Najeriya ba ta da adawa mai ƙarfi, sannan haɗaka tsakanin Peter Obi da Atiku ka iya kawar da Tinubu a 2027

FCT, Abuja - Ana cigaba da yin martani kan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wani mai sanya ido kan zaɓe kuma shugaban Connected Development (CODE), Hamzat Lawal, ya bayyana cewa hukuncin kotun yana akan daidai.

Hamzat ya yi magana kan hukuncin kotun zaben shugaban kasa
Hamzat Lawal ya yi kira ga Atiku da Peter Obi su dunkule waje daya kafin zaben 2027 Hoto: Mr Peter Obi/Hamzat B. Lawal/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da Legit.ng, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Babban Dalilin Da Ya Jawo Wa PDP da Atiku Rashin Nasara Hannun Tinubu Ya Bayyana

"Waɗannan ƙwararrun alƙalai ne masana waɗanda tsawon shekaru suna da gogewa inda su ke kallon hujjoji da idon basira."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Farfagandar labaran ƙarya na soshiyal midiya ba za su yi tasiri akan hukuncin kotun ba. Ni a wajena, ina tunanin doka a kodayaushe za ta yi nasara."

Sai dai, ya yi nuni da cewa lokacin da aka ba masu shigar da ƙara su kammala shirinsu, ya yi tasiri wajen shirinsu wanda hakan ya sanya suka samu kura-kurai.

Wacce shawara Lawal ya ba Atiku, Peter Obi?

Lawal ya buƙaci masu shigar da ƙarar, Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da Sanata Rabiu Kwankwanso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), su koma su haɗa kai waje guda domin kawar da Shugaba Tinubu da APC a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Taya Shugaba Tinubu Murnar Samun Nasara a Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

A kalamansa:

"Ina tunanin suna buƙatar su ajiye girman kai da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su dubi ƴan Najeriya sannan su samar da sabbin ra'ayoyi waɗanda za su ƙalubalanci Tinubu da su."
"Idan suka cigaba a haka, Tinubu zai cigaba da yin nasara a kansu, sannan ya sake ba su kashi a zaɓe mai zuwa."

Alkalai Sun Caccaki Lauyoyin Peter Obi a Kotu

A wani labarin kuma, lauyoyin Peter Obi ba su ji da daɗi ba a lokacin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta zartar da hukuncinta.

Ɗaya daga cikin alƙalan ta caccaki lauyoyin Peter Obi kan rashin gabatarwa da kotun gamsassun hujjoji kan ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu da wanda su ke karewa yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng