Tinubu: Hukumar PSC Ta Umarci DIG 4 Su Gaggauta Yin Ritayar Dole

Tinubu: Hukumar PSC Ta Umarci DIG 4 Su Gaggauta Yin Ritayar Dole

  • Gwamnatin shugaba Tinubu ta sallami mataimakan sufetan yan sanda na ƙasa 4 kuma ta maye gurbinsu
  • Hukumar PSC ta umarci DIG huɗu, wadanda ke sama da sabon muƙaddashin IGP na ƙasa, su yi ritayar dole
  • A cewar kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, sun yi tsammanin manyan jami'an zasu aje aiki da kansu amma har yanzu shiru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta ƙasa (PSC) ta umurci mataimakan sufeto janar na rundunar ‘yan sanda hudu su gaggauta yin ritayar dole.

Manyan jami'an ‘yan sandan da umarnin ya shafa sun hada da Dan-Mallam Mohammed, Moses Ambakina Jitiboh, Hafiz Mohammed Inuwa da kuma Adeleke Adeyinka Bode.

Hukumar jin daɗin 'yan sanda ta sallami DIG huɗu.
Tinubu: Hukumar PSC Ta Umarci DIG 4 Su Gaggauta Yin Ritayar Dole Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar PSC ta ƙasa, Ikechukwu Ani, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Litinin a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

To fah: Za a runtuma kame a wata jiha, 'yan bindiga sun sheke dan sanda, sun sace bindiga da hularsa

Ya ce hukumar kula da harkokin rundunar 'yan sandan Najeriya ta ba su wannan umarnin ne bisa karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, umarnin ya yi daidai da jadawali na Uku, sashe na 1 M, sakin layin A da B na kundin tsarin mulki 1999, wanda aka ƙarfafa da sashe na 6 na dokokin PSC 2001, sakin layi na a, c, d, e, da f.

Ya bayyana cewa umarnin ya zama tilas saboda PSC ta yi tsammanin waɗannan DIG din da suka kasance manya a matsayi kafin mukaddashin IGP, Kayode Egbetokun, za su yi ritaya bisa radin kansu.

Mista Ani ya ce:

"Bayan shugaban ƙasa ya naɗa muƙaddashin sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, ranar 19 ga watan Yuni, 2023, hukumar ta yi tsammanin mataimakan IG zasu bi al'adar rundunar 'yan sanda ta ƙasa."

Kara karanta wannan

Aiki ya fara: Daga zuwa, Ganduje ya yi sabbin nade-nade a kwamitin NWC na APC

"PSC ta sa ran ganin waɗannan DIGn, waɗanda suna sama da sabon IGP, zasu bi al'ada bisa raɗin kansu su rubuta takardar aje aiki."
"Bayan jira na tsawon lokaci ba tare da wani daga cikinsu ya yi ritaya ba, hukumar ta yanke shawarar sallamar su ta tilas, domin a kiyaye da’a, wanda shi ne ginshikin rundunar."

Ya ƙara da cewa wannan matakin zai kuma dakile koma bayan da za a iya samu, wanda ke da illa ga ƙarfin ikon sufeto Janar na kasa (IGP).

PSC ta naɗa sabbin DIG

Bayan haka, hukumar PSC ta amince da naɗa sabbin mataimakan Sufetan yan sanda huɗu, waɗanda zasu maye gurbin DIG bayan majalisar gudanarwa ta sahale naɗinsu.

Sabbin DIG din sun hada da Ibrahim Sani Ka’oje, Daniel Sokari Pedro, Ayuba Ekpeji da kuma Usman Nagogo, kamar yadda jaridar Guardian ta tattaro.

Kwamishinan Anambra Ya Bai Wa Yar Sanda Kyautar N250,000

A wani labarin na daban Kwamishinan 'yan sanda ya bai wa jami'ar 'yan sanda mace kyautar N250,000 bisa nuna gaskiya da rikon amana a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

A wajen gabatar da kyautar tsabar kuɗin ga yar sandan ranar Jumu'a, Kwamishinan ya yabawa Insufekta Charity bisa riƙo da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel