“Ban Taba Gani Ba”: Jami'ar Soja Mace Ta Dauki Juna Biyu, Ta Baje Kolin Katon Cikinta a Bidiyo

“Ban Taba Gani Ba”: Jami'ar Soja Mace Ta Dauki Juna Biyu, Ta Baje Kolin Katon Cikinta a Bidiyo

  • Wata jami'ar soja ta samu juna biyu sannan ta baje kolin katon cikinta a TikTok domin mabiyanta su gani
  • Kyakkyawar sojar, Kaxandre, tana aiki ne da rundunar sojin Amurka, kuma tana sanye da inifam dinta a cikin hadadden bidiyon
  • Wasu mutane da suka ga Kaxandre da cikin da take dauke da shi sun ce wannan ne karo na farko da suke ganin soja mai ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata jami'ar soja mace da ke dauke da juna biyu ta baje kolin katon cikinta a wani bidiyon TikTok.

A wani bidiyo da Kaxandre ta wallafa, jami'ar sojar ta nunawa mabiyanta yadda ta kware a fannin rawa da katon cikinta.

Macen soja dauke da juna biyu
“Kina Da Jarumta”: Macen Soja Ta Dauki Juna Biyu, Ta Baje Kolin Katon Cikinta a Bidiyo Hoto: TikTok/@kaxandre7.
Asali: TikTok

Kaxandre tana sanye da kayan sojoji lokacin da ta bayyana a bidiyon, wanda a yanzu ya samu mutum miliyan 3.8 da suka kalla.

Kara karanta wannan

Mai Da Tsohuwa Yarinya: Yadda Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu

Mai ciki da ke aiki da rundunar sojin Amurka ta nunawa duniya cikinta

A bidiyon, ta daga kayanta domin nuna cikin nata wanda ya girma ya yi kato. Ta kuma taka rawa, inda ta ja hankalin mabiyanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu bidiyoyin a shafinta na TikTok sun kuma nuno ta a gida yayin da take dauke da cikin.

Mabiyanta da dama sun bayyana cewa basu taba ganin jami'ar soja mace da ciki ba a rayuwarsu.

Sauran sun bayyana ta a matsayin kyakkyawa sannan sun karfafa mata gwiwa cewa sun fada a tarkon sonta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da jami'ar soja mace ta baje kolin cikinta

@user1500283167589 yace:

“Wannan ne karo na farko da nake ganin jami’ar soja mai ciki.”

@fedoo07 ta ce:

“Oh antina, na dade ban gan ki ba.”

Kara karanta wannan

Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

@doricereginestlou ta ce:

“Ina farin cikin ganin mace mai ciki sakayau, Allah yasa ki haifi dan kirki.”

@Magareth Sinais 393 ta yi martani:

"Allah ya yi maki rakiya a wannan rana yar'uwa."

@Friday Daniel58 ya ce:

"WOW, karo na farko da nake ganin soja dauke da da. Allah ya sauke ki lafiya."

Mai POS ta fashe da kuka bayan kwastoma ya gudu mata da waya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata mai POS ta shiga tasku sannan ta zub da hawaye bayan wani kwastoma ya sace mata wayarta.

A cewar matashiyar wacce aka dauka a bidiyo, ta ajiye wayar a kan teburinta yayin da take kula da kwatoman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel