“Sai Na Haife Dana”: Miji Ya Dirka Wa Kanwar Matarsa Ciki, Ta Ce Ba Za Ta Zubar Ba

“Sai Na Haife Dana”: Miji Ya Dirka Wa Kanwar Matarsa Ciki, Ta Ce Ba Za Ta Zubar Ba

  • Wata matashiya ta yadu a soshiyal midiya bayan mijin yayarta ya dirka mata ciki yayin da take zama tare da su
  • Da take kare kanta, matashiyar ta bayyana cewa yayar tata ce ta nemi ta hadu da mijinta domin hana shi cin amanarta
  • Masu amfani da soshiyal sun bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon inda wasu da dama suka nuna rashin jin dadinsu

Wani labari ya yadu a soshiyal midiya game da wata yar Najeriya da ta bukaci kanwarta ta kwanta da mijinta domin hana shi neman matan banza a aje.

Matashiyar mai suna Onyiye ta yi ikirarin cewa yayar tata ta bukaci haka ne yayin da take dauke da juna biyu kuma bata iya kwanciya da mijinta.

Miji ya dirkawa kanwar matarsa ciki
“Sai Na Haife Dana”: Miji Ya Dirkawa Kanwar Matarsa Ciki, Dirama Ta Barke Hoto: @ojiugonwa/Twitter.
Asali: TikTok

A cewar Onyinye, ta samu ciki da farko bayan ta kwanta da mijin yayarta sannan ta zubar da cikin.

Kara karanta wannan

"Ta Ki Yarda Ta Tsufa": Hotunan Wata Mata Mai 'Ya'Ya 7 Da Jikoki 5 Sun Janyo Cece-Kuce a Intanet

Ta yi ikirarin cewa ta sake zubar da ciki sau biyu bayan wannan kafin ta yanke shawarar barin na ukun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, yayar tata bata ji dadin lamarin ba inda ta koreta daga gidan, tana mai barazanar kwace shagon kwaliyyar da ta bude mata.

Onyinye, wanda ke tsoron rasa rayuwarta yayin zubar da ciki, ta nemi taimakon wasu mutaned kan su yi wa yayar tata da mijinta magana.

Sai dai kuma, da suka isa gidan yayar tata, sai suka tarar da barazana da tashin hankali daga wajen ma'auratan.

Jama'a sun yi martani

Labarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, inda mutane da dama suka nuna kaduwa da jin haushin halin yar uwar da mijin nata.

@Nithsmit ta yi martani:

"Akwai bukatar yarinyar ta kai lamarin gaban mutanenta.
"Ya kamata su maka mutumin kara kan barna da ya yi, ya kamata yarinyar ta maka su a kotu kan illar da suka mata."

Kara karanta wannan

“Iyayena Sun Nemi Na Bar Masu Gidansu”: Matashiya Ta Koka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Dankara Mata Ciki

@Emeka _firstsonta yi martani:

"Kada yarinyar ta zubar da cikin. Ya kamata ta kai karar lamarin ma'aikatar harkokin mata. 5, F.S.P Avenue, Independence Layout, Independence Layout, Enugu, Enugu.”

@SirJaby ya ce:

"Wato na ji sunan jihar Enugu a hirarsu. Matashiyar na iya kai kara ma'aikatar harkokin mata. Za su daura daga nan."

Kalli wallafar a kasa:

Saurayi dan shekara 19 zai yi wuff da budurwa yar 17

A wani labari na daban, mun ji cewa wani saurayi mai shekara 19 a duniya yana shirin angwancewa da kyakkyawar budurwarsa yar shekara 17.

Bidiyoyin kafin aurensu ya yadu a soshiyal midiya kuma za a daura masu aure nan da yan watanni kadan masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel