Kyakkyawar Soja Ta Wallafa Bidiyon Da Ke Nuna Yawan Kudin Da Ta Samu a Matsayin Sojar Amurka a 2022

Kyakkyawar Soja Ta Wallafa Bidiyon Da Ke Nuna Yawan Kudin Da Ta Samu a Matsayin Sojar Amurka a 2022

  • Wata matashiyar sojar Amurka ta nuna a wani bidiyo cewa tana samun fiye da $100,000 (N45,005,000) a matsayin albashi da sauran alawus a matsayin jami'a
  • A zangon farko na shekarar, ta samu kudin shiga da ya kai $35,841.72 (N16,130,566.09) da albashinta na watan Mayu $26,725.44 (N12,027,784.27)
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun so sanin matakin da take kai a rundunar sojin da har take samun kudaden sannan wasu sun nuna sha'awarsu ga aikin

Wata bakar fata mai sun @diaryofdom__, ta garzaya soshiyal midiya don sanar da mutane yawan kudaden da ta samu a matsayin sojar Amurka a shekarar 2022.

A wani dan gajeren bidiyo da ta wallafa, ta jeranto albashinta na wata-wata. A watan Janairu ta samu $8,836,59. A watan da ya biyo baya, ta samu irin haka.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo da Ragowar ‘Yan wasa 10 da Suka fi Kowa karbar Albashi a 2023

Jami'ar soja
Kyakkyawar Soja Ta Wallafa Bidiyon Da Ke Nuna Yawan Kudin Da Ta Samu a Matsayin Sojar Amurka a 2022 Hoto: TikTok/@diaryofdom
Asali: UGC

Kudaden shiga a matsayin sojar Amurka

A watannin Maris, Afrilu da Mayu, ta samu $8,986.35 (N4,044,306.82), $9,182.19 (N4,132,444.61) and $26,725.44 (N12,027,784.27).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sune Yuni ($9,182.19), Yuli (&11,458.15 ), Agusta ($9,587.19), Satumba ($9,587.19), Oktoba ($9,587.19), Nuwamba ($9,587.19), da Disamba ($9,587.17).

Alkalman biya ya nuna cewa:

"Rundunar sojin Amurka na biyan matsakaicin ma'aikatanta akalla $65,352 a shekara. Albashin rundunar sojin Amurka ya kai daga $34,460 zuwa $122,608."

Matashiyar ta bukaci mutane da su je su tabbatar idan karya take yi. A wani bidiyon, ta yi bayanin wani bangare na abun da ta samu a shekarar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

KnoMotionNupe ya ce:

"Wannan harda BAH BAS kuma a yi la'akari da dadewar mutum a aiki. Mu yi magana ta gaskiya wannan ba shine abun da kowa ke karba ba."

Kara karanta wannan

EFCC ta Fallasa Cuwa-Cuwar Naira Biliyan 13 a Harkar Tallafin Fetur a Shekaru 5

Ariana ta ce:

"Toh me kike son fada mani shine cewa ina bukatar kaso."

GsxrSquid_J ya ce:

"Kuna mamakin dalilin da yasa a kodayaushe NCOs ke zabura yayin da jami'ai ke farin ciki. Wannan shine dalili."

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya tara jama'a domin yin addu'an godiya ga Allah sakamakon kera wata mota mai siffar G-Wagon da ya yi.

Matashin ya tara jama'ar kauyensa a jahar Enugu domin nuna murna kan wannan gagarumin nasara da ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng