Mai Da Tsohuwa Yarinya: Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu

Mai Da Tsohuwa Yarinya: Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata tsohuwa da ke da baki-baki a fuskarta ta sauya gaba daya bayan an tsantsara mata kwalliyar zamani a fuska
  • Shekarun matar 81 a duniya, kuma tana kwalliya ne don halartan shagalin bikin jikarta
  • Yadda ta koma bayan kwalliyar ya shayar da masu amfani da TikTok mamaki saboda ta dawo shar da ita sannan fuskar ta yi sumul

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya da ke aikin kwalliya ta dauki lokacinta da kyau wajen fito da tsantsar kyawun wata tsohuwa.

Matar, wacce shekarunta 81 a duniya ta cika da murna bayan an kammala kwalliyan saboda ta kara kyau sannan an yi mata abun da ake kira da 'mai da tsohuwa yarinya'.

Tsohuwa ta zama yar budurwa bayan an mata kwalliya
Mai Da Tsohuwa Yarinya: Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@nikzybeauty
Asali: TikTok

Matar da aka cancarawa kwalliyar tana shirin zuwa wajen daurin auren jikarta ne.

Mai kwalliya ta sauya fuskar tsohuwa yar shekaru 81

Kara karanta wannan

Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Sai dai kuma da taimakon abubuwan da mai kwalliyar ta shafa mata, sai ga shi baki-bakin da ke fuskarta ya boye sannan ta koma sumul da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ta kammala, mai kwalliyar ta sanyawa tsohuwar bakin gashi dan kanti, wanda yasa ta kara zama matashiya.

Masu amfani da TikTok da suka kalli bidiyon sun yarda cewa abun ya kayatar, sannan sun jinjinawa mai kwalliyar da aikin da ta yi. @nikzybeauty ce ta wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@SHOPWITHLAVIE_ ta ce:

"A karshe wata ta yi kwalliya daidai da shekaru."

@Erykah ta ce:

"Tana da fata sumul a shekarunta. Kawai dai kalar da ke kai ne."

@Temienor Ejiro ta ce:

"Wow! 81? Tana da kyau."

@user9123040366819 ta ce:

"Kaka. Muna sonki. Godiya ga wannan mai kwalliyar."

@Sexyjulie ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari’a Ta Bai Wa Magidanci Masauki a Gidan Yari Kan Lakadawa Tsohuwar Matarsa Duka

"Tana da kyau a 81. Sannan wannan kwalliyar ta hadu."

@efdbeauty ta ce:

"Wannan shine abun da nake kira daidai shekaru."

@Naima Zubeir ta ce"

"Wow! Ta tsufa, tana walwali."

Bidiyon Bahaushiya tana tikar rawa ya girgiza intanet

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa Bahaushiya ta burge masu amfani da soshiyal midiya saboda yanayin rawar da ta yi a wajen wani taro.

A bidiyon da aka wallafa a TikTok wanda ya samu mutum sama da miliyan da suka kalla, an gano matashiyar tana rawa tare da girgiza kwankwasonta yayin da wani kida ke tashi daga kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel