Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata budurwa Bahaushiya ta shahara a soshiyal midiya bayan ta baje kolin rawanta a wajen wani taro wanda aka kwasa a bidiyo
  • Matashiyar da ke sanye da doguwar rigar atampa, ta juyawa kamara baya yayin da ta dunga girgiza kwankwasonta
  • Yanayin rawarta ya burge mutane da dama inda suka soki dayar budurwar da ta shigo fage don taya ta

Wata budurwa Bahaushiya ta burge masu amfani da soshiyal midiya saboda yanayin rawar da ta yi a wajen wani taro.

A bidiyon da aka wallafa a TikTok wanda ya samu mutum sama da miliyan da suka kalla, an gano matashiyar tana rawa tare da girgiza kwankwasonta yayin da wani kida ke tashi daga kasa.

Matashiya na tikar rawa
Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Yayin da Ta ‘Girgiza Kwankwaso’ Wajen Rawa, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @abibamohammed357
Asali: TikTok

Matashiyar budurwar wacce ta sanya atampa dinkin doguwar riga, ta juyawa kamara baya yayin da ta fara girgiza kwankwasonta cikin sauri.

Kara karanta wannan

Mai Da Tsohuwa Yarinya: Yadda Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu

Wata matashiya ta shigo filin domin tayata taka rawa amma sam rawanta bai burge masu kallo ba. Hatta da MC abun ya yi masa dadi har ya fara jinjina mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun soki dayar budurwar da ke sanye da bulun atampa kan rufe masu wuri da ta yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Obaapa addepa 390 ya ce:

"Wanene kuma ya kalla fiye da sau 50 kamar yadda na yi.. hmm karfinta ya sha kan na karshen."

Black skin ta ce:

"A kodayaushe mai karamar mazaunin ne ke son shigewa gaba, yar'uwata je ki samu wuri ki zauna."

user324437734477 ya ce:

"A fada ma almakashin nan da ta shigo a karshe da ta je ta huta don Allah."

asianbarbie ta ce:

"Ban taba hango zuwan ta biyun ba."

Kara karanta wannan

Kitimurmura Yayin Da Mahaifiya Ta Rikice Bayan Ganin 'Yarta Budurwa A Makale Da Mijinta, Bidiyon Ya Jawo Kace-Nace

Legitforex ya ce:

"Daga ina dayan aljanar ta shigo."'

Jami'ar soja mace ta baje kolin cikin da take dauke da shi

A wani labari na daban, mun ji cewa wata jami'ar soja mace da ke dauke da juna biyu ta baje kolin katon cikinta a wani bidiyon TikTok.

A wani bidiyo da Kaxandre ta wallafa, jami'ar sojar ta nunawa mabiyanta yadda ta kware a fannin rawa da katon cikinta.

Kaxandre tana sanye da kayan sojoji lokacin da ta bayyana a bidiyon, wanda a yanzu ya samu mutum miliyan 3.8 da suka kalla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel