'Yan Addinin Gargajiya Sun Samu Karin Karbuwa, an Ware Musu Ranar Biki da Hutu a Jihohin Kudu 4

'Yan Addinin Gargajiya Sun Samu Karin Karbuwa, an Ware Musu Ranar Biki da Hutu a Jihohin Kudu 4

  • Jihohi hudu a kudu maso yammacin Najeriya sun ayyana ranar Litinin 21 ga watan Agusta a matsayin ranar hutun aiki don bikin murnar ranar Isese ta 2023
  • Jihohin Kudu maso Yamma da suke gudanar da wannan biki na musamman sun hada da Legas, Oyo, Osun, da Ogun
  • Gwamna Sanwo-Olu na Legas da takwarorinsa sun bayyana mahimmancin kiyaye al'adun Yarbawa da samar da hadin kai da jituwa a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Domin tunawa da ranar Isese ta 2023, akalla jihohi hudu a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun ayyana ranar Litinin 21 ga watan Agusta a matsayin ranar hutun aiki ga ma’aikatan gwamnati.

An kebe ranar Isese a mafi yawan jihohin Kudu maso Yamma domin gudanar da bukukuwan al'adu na Yarabawa na asali da tushe da kuma kiyaye al'adun kabilar.

Kara karanta wannan

Neman Alawus: Bidiyon Tubabbun Yan Boko Haram Suna Zanga-Zanga a Borno, Sun Rufe Hanya

A gwamnatin Najeriya, ana ba da hutun ranakun bukukuwan addini, ciki har da Kirsimeti da kuma Sallah a duk shekara.

Addinin gargajiya ya sake dawowa a Kudu
Gwamnonin da suka amince da addinin gargadjiya | Hoto: @jidesanwoolu, @Yorubaness, @seyiamakinde
Asali: Twitter

Ga jerin jihohin da suka ayyana ranar Litinin ranan hutun ma’aikata:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  1. Jihar Legas
  2. Jihar Oyo
  3. Jihar Osun
  4. Jihar Ogun

Ranar Isese: Abin da gwamnonin jihohin suka ce

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce ya ayyana ranar hutu ne domin murnar wannan rana ta musamman da kuma jaddada aniyarsa na ci gaba da ba da gudunmawar da ta dace ga addinin gargajiya a jihar Legas.

Ya kara da cewa gwamnatin sa na da sha’awar bunkasa al’adun ’yan asalin jihar Legas tare da kiyaye martabar al’adun da kabilar.

Hakazalika, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da ranar 20 ga watan Agustan kowacce shekara a matsayin ranar Isese.

Gwamnan ya bukaci a yi amfani da wannan biki wajen addu’ar zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ce shawarar da aka yanke na ware ranar Isese don a huta a matsayin ci gaba da mutunta al’ada tare da tabbatar da dorewar hadin kai da daidaito a tsakanin manyan addinai uku a jihar.

An cika burin ‘yan addinin gargajiya

A tun farko, kungiyar Iseselagba ta Kasa (yan addinin gargajiya) a ranar Litinin sun mika bukatarsu ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya don ba wa yan kungiyar hakikinsu a matsayin yan kasa, Punch ta rahoto.

Kakakin kungiyar (Awise) a Jihar Ekiti, wanda ya ce addinai uku ne a Najeriya - kiristanci- musulunci - da na gargajiya, ya ce an banzatar da yan addinin gargajiya wajen rabon makuman gwamnati.

Lawal, wanda ya wanda ya zanta da manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ya yi kira ga gwamnati "ta rage mukaman da take ba wa kiristoci da musulmai zuwa ga yan addinin gargajiya."

Kara karanta wannan

Komai Ya Lafa, Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin ‘Hutun’ da Aka Biya Sanatoci

Asali: Legit.ng

Online view pixel