Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci

Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci

- Abinda namiji zai yi ya azabtar da matarsa shine yayi tarayya da 'yar uwarta, don na gwada kuma na tabbatar, inji wani mutum

- Mutumin mai suna Maduakor Wiseman Jesus, ya yi tunkaho da karshen cutarwar da yayi wa matarsa har ta tafi ta bar shi da jariri

- Ya shawarci maza cewa idan suna so su yi maganin matansu su yi tarayya da 'yan uwansu, ba za su taba yafewa ba har abada

Babu abinda yafi yi wa kowacce mace radadi kamar mijinta ya ha'inceta da 'yar uwarta.

Wani mutum dan Najeriya mai yara 2, mai suna Maduakor Wiseman Jesus ya ce babbar hanyar da namiji zai yi maganin matarsa idan ta bata masa rai shine yayi tarayya da 'yar uwarta.

A cewarsa, "Idan matarka ta bata maka rai, kuma kana so ka azabtar da ita, ka fara tarayya da 'yar uwarta ta jini, kuma ka tabbatar ta gano, yafi musu radadi fiye da kayi tarayya da wasu a waje".

Kamar yadda ya rubuta, matarsa ta bar shi da jaririya bayan ta gano yana tarayya da kanwar ta.

"Ba na wallafa abinda na san ba ya aiki. Za ta karasa rayuwarta cikin bala'i da tashin hankali. Na kasance ina ha'intar mata ta da kanwarta.

"Bayan ta gano, sai na bata hakuri tun da na gano wannan hanyar. Ta tafi ta barni da jaririya. Bata sake waiwayata ba, muka rabu.

"Ta haka na gano cewa wannan al'amarin ya fi komai azabtar da su. Ina so in sanar da ku wannan dabarar ne, a matsayina na mutum mai wayau" a cewarsa.

KU KARANTA: Ku kara hakuri da mu, ba mu yi muku abinda ya dace ba - Buhari ga 'yan Najeriya

Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci
Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci. Hoto daga Maduakor Wiseman Jesus
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Mutum 6 sun harbu da cutar korona a makarantar sakandare

A wani labari na daban, wani mutum mai suna Mlekeleli Masondo, dan asalin South Africa, ya yi wata wallafa a shafinsa na Facebook, ta yadda yayi amfani da shafin bogi na kafar sada zumuntar zamani, har ya gano matarsa tana ha'intarsa.

Kamar yadda Masondo ya wallafa, ya yi amfani da sunan bogi, har matarsa ta amince da za su fita yawon shakatawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce ta dade tana hanasa hakkinsa na aure domin ta tattala wa saurayinta, ya kwashi gara a ranar farko da za su hadu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel