Mahaifin Yaron Da Ya Samu Sakamako Mafi Kyau A WAEC Ya Fadi Yadda Ya Taimake Shi

Mahaifin Yaron Da Ya Samu Sakamako Mafi Kyau A WAEC Ya Fadi Yadda Ya Taimake Shi

  • A sakamakon jarrabawar WAEC na 2023, wani yaron mai suna Isa Salmanu ya samu sakamako mafi kyau na A1 a dukkan darussa tara
  • Isa dalibi ne a makarantar Premier Academy da ke Lugbe a Abuja inda aka bayyana shi a matsayin tauraron shekarar 2023 na makarantar
  • Isa ya kuma samu maki 347 a jarrabawar JAMB na 2023, mahaifinsa ya yi tsokaci ga Legit.ng kan yadda su ka kara masa karfin gwiwa

FCT, Abuja - Mahifin Isa Salmanu, yaron da ya samu sakamako mafi kyau a jarrabawar WAEC, Musa Salmanu ya bayyana yadda ya karfafi gwiwar dan nasa.

Hukumar jarrabawa ta WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar dalibai a ranar Litinin 7 ga watan Agusta inda Isa Salmanu ya samu sakamako mafi kyau (A1) a dukkan darussa tara.

Kara karanta wannan

Halin Kirki Ya Yi Rana, Sanata Ya Kare Malaminsa Wajen Tantance Ministocin Tinubu

Mahaifin yaron da ya zama tauraro a WAEC ya yi magana kan dan nasa
Isa Salmanu Yaron Da Ya Samu Sakamakon Mafi Kyau A WAEC. Hoto: Nasir Aminu Musa.
Asali: Facebook

Wannan kokari na matashin ya samu yabo daga jama’a da dama musamman a kafafen yada labarai.

Meye mahaifin yaron yace kan sakamakon WAEC?

Yayin da ya ke magana da Legit.ng, mahaifin yaron, Musa Isa Salmanu wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma tsohon dan majalisar jihar Kaduna ya bayyana yadda su ke ba wa yaron kwarin gwiwa a gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun yaron ya na karami ya fahimci shi na daban ne kuma tun ya na makarantar firamare ya ke samun sakamako na daban a cikin ‘yan uwansa dalibai.

Ya fadawa Legit.ng cewa:

“Kullum muna kara masa karfin gwiwa, mun fada masa cewa mun yarda da shi, mun tabbatar masa da cewa shi mai kwazo ne."

Isa har ila yau, ya samu maki 347 a jarabawar share fagen shiga jami'a ta JAMB da aka sake a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Shin tun a baya haka yaron ya ke?

Musa Isa ya kara da cewa:

“Ya na da tarihin nasarori a jarrabawar da ya ke rubutawa tun ya na makarantar firamare.
“Ya taba samun tallafin karatu na kamfanin NNPC da Shell da dauki nauyi, a lokacin an dauki masu kwazo a makarantin firamare kuma ya na ciki.
"Dalilin haka, ina jin cewa zai zama na daban, na ji dadin yadda ya samu wannan sakamako.”

WAEC ta sake sakamakon jarrabawar 2023

A wani labarin, Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC ta saki sakamakon jarrabawar shekarar 2023.

Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, Patrick Areghan yayin ganawa da manema labarai a Yaba da ke Legas a ranar 7 ga watan Agusta.

Ta bayyana cewa daga cikin dalibai 1,613,733 da suka zauna jarabawar, an rike sakamakon dalibai 262,803 kan zargin satar jarabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel