Babagana Zulum Ya Rabawa Magidanta 13,000 Kayan Abinci a Jihar Borno

Babagana Zulum Ya Rabawa Magidanta 13,000 Kayan Abinci a Jihar Borno

  • Gwamnan Babagana Umar Zulum na jihar Borno, ya rabawa magidanta 13,000 da ke karamar hukumar Gwoza kayayyakin abinci
  • Zulum ya dauki wani matakin ne don ganin ya tallafawa wadanda rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram ya jefa cikin wani yanayi
  • A yayin rabon kayan abincin wanda gwamnan ya jagoranta da kansa, an bai wa kowane gida buhu daya na shinkafa da kuma na masara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwoza, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba kayayyakin abinci ga magidanta 13,000, wadanda mafi akasarinsu rikicin Boko Haram ya shafa a karamar hukumar Gwoza da ke jihar.

Hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar ranar Litinin a Maiduguri babban birnin jihar.

Leadership ta ruwaito cewa an yi rabon kayayyakin ne a ranar Lahadi, a harabar fadar Sarkin Gwoza, Shehu Idrissa Timta.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Farfesa Njodi a Matsayin SSG, Ya Kaddamar Da Kwamitin Masu Ba Shi Shawara

Zulum ya yi rabon kayayyakin abinci a Gwoza
Gwamna Zulum ya rabawa magidanta 13,000 kayan abinci a Gwoza. Hoto: The Governor Of Borno State
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum ya bai wa kowane gida buhun shinkafa daya da na masara daya

Zulum dai ya je karamar hukumar ta Gwoza ne a ranar Asabar, inda a yayin hakan ya kai ziyarar ba zata babban asibitin garin cikin tsakar dare.

Bayan kammala duba halin da asibitin yake ciki, Gwamna Zulum ya kuma ba da umarnin a dauki matakan gyare-gyare cikin gaggawa.

Washegari kuma Zulum ya jagoranci rabon kayayyakin abincin da kansa, inda kowane gida daga cikin 13,000 ya samu buhun shinkafa daya da na masara ma guda daya.

Zulum ya samu rakiyar wasu daga mukararrabansa

A yayin wannan gagarumar ziyara da Babagan Zulum ya kai karamar hukumar ta Gwoza, ya samu rakiyar wasu daga cikin mukarraban gwamnatin jihar Borno.

Daga ciki akwai Barkindo Mohammed Saidu, sabon Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), wanda tare da shi aka yi rabon kayayyakin abincin, kamar yadda aka wallafaa shafin gwamnan na Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Gwamnan tare da sabon Daraktan, sun tabbatar da cewa mutanen da suka cancanta ne aka bai wa kayayyakin abincin.

Haka nan Zulum ya samu rakiyar dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazabar Marte, Monguno, da Nganzai, Injiniya Bukar Talba, tare da karin wasu mukarraban gwamnatin jihar.

Zulum ya haramta sana’ar Jari Bola a jihar Borno

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton matakin da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya dauka na haramta sana’ar jari bola a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin kare masu sana’ar daga hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel