Shugaba Tinubu Ya Kira Alkalin Alkalai Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasa? APC Ta Bayyana Gaskiya

Shugaba Tinubu Ya Kira Alkalin Alkalai Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasa? APC Ta Bayyana Gaskiya

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan zargin cewa Shugaba Tinubu ya tattauna da alƙalin alƙalai na ƙasa, Olukayode Ariwoola, a wayar tarho
  • Felix Morka, kakakin jam'iyyar na ƙasa ya bayyana zargin da Jackson Ude na jam'iyyar Labour Party ya yi a matsayin zancen ƙarya
  • Morka, wanda ya ce jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu sun lashe zaɓen, ya zargi Ude da yin kalaman ƙarya marasa tushe ballantana makama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi martani kan zargin cewa Shugaba Tinubu ya kira alƙalin alƙalai na ƙasa, Olukayode Ariwoola, kan shari'ar zaɓen shugaban ƙasa da ake yi a kotu.

Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC na ƙasa a cikin wata sanarwa da NTA ta wallafa a Twitter, ya bayyana cewa zargin da wani ɗan jam'iyyar Labour Party mai tallata Peter Obi, Jackson Ude, ya yi ne da gangan domin kawo ruɗani.

Kara karanta wannan

Jiki Magayi: Jam'iyyar Peter Obi Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube Kan Farashin Man Fetur, Ta Fadi Abinda Zai Faru Gaba

APC ta musanta zargin Tinubu ya kira Ariwoola
APC ta musanta zargin Tinubu ya kira Ariwoola kan shari'ar zaben shugaban kasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ude, a cikin rubutun da ya yi, ya yi zargin cewa Tinubu ya tattauna da Ariwoola, amma a martanin da Morka ya yi ya zargi ɗan jam'iyyar ta LP da yaɗa ƙarya da ƙarairayi.

Batun tattaunar Tinubu da alƙalin alƙalai ƙarya ce, cewar APC

Morka ya zargi Ude da yaɗa ƙarya da ƙarairayi kan batu mai matuƙar muhimmanci wanda yanzu haka yake a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Morka, Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC sun lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu ba tare da wata tantama ba, saboda haƙa babu dalilin da zai sanya shugaban ƙasar ya kira alƙalin alƙalan kan batun ƙarar da ta ke a gaban kotun.

Jam'iyyar APC ta nuna ƙwarin gwiwarta cewa ƴan Najeriya sun fi ƙarfin su bari ƴan adawa su ruɗe su da zantuttukan ƙarya da su ke yaɗa wa.

Kara karanta wannan

Sakataren Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa Tare Da Ficewa Daga Jam'iyyar, Ya Bayyana Dalilansa

Zaman Jiran Ministocin Tinubu Ya Kare

A wani labarin kuma, majalisar dattawa za ta karanto jerin sunayen ministocin da Shugaba Tinubu zai naɗa a gwamnatinsa.

Majalisar za ta bayyana sunayen ne waɗanda aka daɗe ana jira a zamanta na ranar Laraba, 19 ga watan Yulin 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel