Bankin CBN Na Raba Tallafin Tsabar Kudi N500,000 Ga Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Bankin CBN Na Raba Tallafin Tsabar Kudi N500,000 Ga Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta na yanar gizo sun yi iƙirarin cewa babban bankin Najeriya (CBN) na bayar da tallafin kuɗi naira N500,000 ga ƴan ƙasa
  • Ƴan Najeriya da dama na buƙatar tallafi biyo bayan tsige tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi
  • Wani dandali na binciken gaskiya ya binciki iƙirarin tallafin tsabar kuɗi N500,000 kuma ya yanke hukuncin cewa wannan batun wata hanyar zamba ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wasu rubuce-rubuce a shafin sada zumunta na Facebook, sun yi iƙirarin cewa babban bankin Najeriya (CBN) na bayar da "tallafin bashi" a 2024.

Ana iya samun wasu daga cikin waɗannan rubuce-rubucen a nan da nan.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya damfari mabiyansa $1.3m, ya bayyana wanda ya ba shi umarnin yin hakan

An binciko gaskiya kan tallafin N500k na CBN
Bincike ya nuna cewa CBN bai bayar da tallafin bashi na N500,000 ga yan Najeriya Hoto: Damilola Onafuwa
Asali: Getty Images

La’akari da cewa batun ya yaɗu sosai, wani dandali na binciken gaskiya, Africa Check, ya gudanar da bincike a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan bincikensa, Africa Check ya ce wannan iƙirari ƙarya ce kuma bai fito daga bankin CBN ba.

Dandalin ya bayyana cewa ya binciki ko Shugaba Tinubu ta hannun bankin CBN yana bayar da wani bashi ko kuma bada tallafin rabin miliyan amma babu wata shaida.

Wasu daga cikin tallafin da Tinubu ya sanar

A halin da ake ciki, wani rahoto da cibiyar bincike ta ICIR ta fitar ya ce tsakanin 29 ga watan Mayu, 2023, da 1 ga watan Oktoba, 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da aƙalla tallafi guda tara don rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

A cikin wannan alƙawari, gwamnatocin jihohi 36 sun samu jimillar kuɗi naira biliyan 72 daga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Sai dai kuma, bayan watanni biyar da fitar da kuɗaɗen, gwamnonin jihohin sun ƙi bayyana yadda aka yi da kuɗin ko nuna shaidar abin da suka yi da kuɗin, cewar rahoton Leadership.

Gwamnan CBN Ya Magantu Kan Farashin Man Fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi tsokaci kan farashin man fetur.

Crdoso ya bayyana cewa a wannan shekarar ta 2024, ƴan Najeriya za su saya man fetur a farashi mai arha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel