Masu ba Gwamnan Kano Shawara Sun Doshi 50 Bayan Nade-Naden Sababbin Mukamai

Masu ba Gwamnan Kano Shawara Sun Doshi 50 Bayan Nade-Naden Sababbin Mukamai

  • Mai girma Abba Kabir Yusuf ya fitar da karin sunayen wadanda zai yi aiki da su a matsayin hadimai
  • Gwamnan Kano ya sanar da karin masu bada shawara a kan addini, harkokin kasuwanci da ma’adanai
  • A cikin wadanda aka ba mukaman akwai Usamatu Salga, Rt. Hon. Isyaku Danja da Habibu El-Yakub

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu mutane a matsayin masu taimakawa da kuma ba shi shawarwari.

Sanarwar nadin mukaman ta fito ne daga bakin Sanusi Bature Dawakin Tofa a daren Talatar nan.

Wadannan mutane da Gwamna Abba Kabir Yusuf za su shiga sahun masu bada shawara na musamman kamar yadda doka ta ba shi dama.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta fahimci hakan ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar Kano tayi wa Gwamnan na kara nada wasu hadimai 25.

Kara karanta wannan

An Damke Sarkin Arewa da Mai Dakinsa a Kudancin Najeriya Saboda Alaka da Emefiele

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban mai taimakawa Gwamnan wajen yada labarai ya ce an samu masu bada shawara a kan harkokin addini, sha’anin majalisa da sauransu.

Wadanda aka ba mukamai

1. Kanal Abubakar Usman Garin Malam (mai ritaya) – Mai bada shawara a kan kula da annoba

2. Malam Usamatu Salga - Mai bada shawara a kan harkokin addinai I

3. Hon. Abduljabbar Muhammad Umar - Mai bada shawara a kan hadin gwiwa da kamfanonin kasuwa da zuba hannun jari

4. Hon. Aminu Abba Ibrahim - Mai bada shawara a kan harkar ma’adanan kasa.

5. Injiniya Nura Hussain - Mai bada shawara a kan sha’anin ciniki.

6. Hon. Jamilu Abbas - Mai bada shawara a kan kungiyoyin kasuwanci.

Jamu Yusuf sun samu shiga

7. Hon. Muhammad Jamu Yusuf - Mai bada shawara a kan huldar gida da ketare.

8. Balarabe Ibrahim Gaya - Mai bada shawara a kan tsare-tsaren tallafi na musamman.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

9. Rt. Hon. Isyaku Ali Danja - Mai bada shawara a kan harkar majalisa.

10. Kwamred Baffa Sani Gaya - Mai bada shawara a kan harkokin ‘yan kwadago.

11. Injiniya Abdullahi Shehu - Mai bada shawara a kan tsabtar muhalli.

12. Hon. Umar Musa Gama - Mai bada shawara a kan ciyar da ‘yan makaranta.

13. Hon. Habibu Hassan Elyakub – Mai bada shawara a kan ilmin koyon sana’a.

14. Hon. Jamilu Abubakar Dambatta - Mai bada shawara a kan yada labarai.

15. Hon. Umar Uba Akawu - Mai bada shawara a kan sha'anin ofishin Abuja.

Nadin mukamai a Kano

A cikin kwanakin farko a ofis, an ji labari Mai girma Abba Yusuf ya nada sahun farko na mashawartansa, wannan karo ya sake zabo wasu mutane 15.

Daga baya kuma Gwamnan ya nadawa hukumomin KAROTA, REMASAB da rediyon Kano sababbin shugabanni baya ga wasu hadimai da ya nada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel