An Damke Sarkin Arewa da Mai Dakinsa a Kudancin Najeriya Saboda Alaka da Emefiele

An Damke Sarkin Arewa da Mai Dakinsa a Kudancin Najeriya Saboda Alaka da Emefiele

  • Majalisar Sarakunan Arewa da ke Kudancin Najeriya sun soki kama Sarkin Hausawa a Legas
  • A wani jawabin Jarman Legas, an ji cewa Sarakunan sun yi kira ga DSS da ta fito da Sarkin Hausawa
  • Yarima Shettima ya nesanta Alhaji Aminu Yaro da Godwin Emefiele wanda ake bincike a kan shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Majalisar Sarakunan Arewa da ke yankin kudancin Najeriya ta yi Allah-wadai da tsare Aminu Yaro da har yanzu Hukumar DSS ta ke yi.

Rahoton Daily Trust ya nuna har yanzu Alhaji Aminu Yaro ya na hannun DSS, ana yi masa tambayoyi game da dangantakarsa da Godwin Emefiele.

Basaraken ya shafe kwanaki a jere ba tare da ya ga iyalinsa ba, hukumar tsaron ta rike shi na fiye da na sa’a’o’i 24 da dokar kasa ta jami’ai dama.

Kara karanta wannan

Lauyoyi 60 Sun Yi Taron Dangi, Za Ayi Shari’a da DSS a kan Godwin Emefiele

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele a Park Hyatt New York Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A matsayinsa na Jarman Legas, Yarima Shettima ya fitar da jawabi a makon nan, yana neman alfarmar fito da jagoran ‘Yan Arewan da mai dakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sarkin Hausawa na bukatar lauya da likitoci

Yarima Shettima yana da ra’ayin cewa bai halatta a cigaba da garkame wadannan Bayin Allah ba.

An rahoto Jarman yana neman jami’an tsaron masu fararen kaya su bar Sarkin Hausawa da iyalansa su samu wakilcin Lauya da zai kare su a doka.

Baya ga samun wakilci ta bangaren shari’a, Shettima ya ce Mai martaba Sarkin Hausawa zai bukaci samun kulawar asibiti da damar ganin ‘yanuwa.

Jawabin Jarman Legas

"Hankalin majalisar Sarakunan Arewan ya kai ga cigaba da tsare Sarkin Hausawan Legas kuma shugaban Sarakuna, Alhaji Aminu Idris Yaro da DSS ta ke yi ba tare da wani bayani ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Mun kuma lura cewa ba tare da an ce uffan ba, hukumar DSS tayi kwanaki uku ta na tsare Sarkin Hausawa, wanda kafin yanzu gayyata ake aika masa, shi kuma sai ya gabatar da kan shi.
Mu ‘yan majalisar Sarakunan Arewa mun fahimci an kama Sarkin Hausawa ne saboda dangantakarsu da aka gani wajen binciken tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele.
Majalisar ba ta san da wata alakar abokantaka tsakanin Sarkin Hausawa da Mista Emefiele face irin yadda Emefiele yake da abokai daga cikin Sarakai a ko ina a fadin Duniya gaba daya ba.”

- Yarima Shettima

An ce a daure Yusuf Magaji Bichi

Tsohon Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele zai iya samun ‘yanci daga hannun DSS domin an ji labari kungiyar lauyoyi ta tsoma baki a kan batun a kotu.

Lauyoyi su na so Alkalin kotun tarayya na Abuja ya daure shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi a kurkuku, saboda raina kotu wajen cigaba da tsare Emefiele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel