Yan Sanda Sun Kai Samame Jami'ar Jihar Enugu, Sun Tattara Dalibai

Yan Sanda Sun Kai Samame Jami'ar Jihar Enugu, Sun Tattara Dalibai

  • Dakarun hukumar 'yan sanda sun kai mamaya jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu da yammacin ranar Jumu'a, sun kama ɗalibai maza da mata
  • Shugaban ɗaliban jami'ar ya roki gwamnan Enugu ya taimaka ya sa baki a sako yan uwasu ɗalibai daga inda aka tsare su
  • Ya ce 'yan sanda suna azabtar da su, sun sako ɗalibai mata bayan kwace musu waya, sun tafi da ɗalibai maza

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Enugu state - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Enugu sun kai mamaya jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu (ESUT) kuma sun kama ɗaliban makarantar sun tafi da su.

Rahoton Punch ya tattaro cewa dakarun 'yan sanda sun kutsa kai cikin harabar jami'ar da yammacin ranar Jumu'a yayin da mutane ke zaman bin dokar zaman gida ta ƙungiyar 'yan ta'adda IPOB a sassan Enugu.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Bindiga, Sun Halaka Ɗaya Sun Kamo 2 a Jihar Arewa

Jami'ar Kimiyya da fasaha ta jihar Enugu.
Yan Sanda Sun Kai Samame Jami'ar Jihar Enugu, Sun Tattara Dalibai Hoto: punchng
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar ɗaliban jami'ar ESUT Donatus Okolieuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai yau Asabar, ya ce ba su ji daɗin abinda 'yan sanda suka yi ba.

Ya ce yan sandan sashin yaƙi da kungiyoyin asiri na rundunar yan sanda Enugu ne suka shigo, suka tattara ɗaliban jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okolieuwa ya yi kira gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya tsoma baki cikin wannan rigimar domin ɗaliban da aka kama su shaƙi iskar 'yanci.

A rahoton Sahara Reporters, shugaban ɗaliban jami'ar ESUT ya ce:

"Muna kira ga mai girma gwamnan mu mai tausayi, Dakta Peter Ndubuisi Mbah ya sa baki a wannan lamarin, ya yi amfani da karfin ofishinsa wajen ganin an sako 'yan uwanmu ɗalibai."
"Ɗaliban nan ba su cancanci azabtarwa mai raɗaɗi ta rashin tausayi ba, ga hukunci mai zafi kan wani ɗan karamin dalili."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Amarya Yar Shekara 21, Maimunatu Ta Caka Wa Angonta Wuka Har Lahira Kan Karamin Abu a Bauchi

Wane hali daliban da aka kama suka shiga?

Ya ƙara da cewa an azabtar da ɗaliban makarantar da cin mutunci kala-kala ciki harda ɗalibai mata, waɗanda daga bisani aka sako su bayan kwace wayoyi da karikitansu.

Mista Okolieuwa ya ce bayan sako mata, 'yan sandan sun yi gaba da ɗalibai maza kuma da ya tuntuɓi shugaban jami'a (VC) da sauran muhukunta sun tabbatar masa babu hannunsu a lamarin.

A halin yanzu, duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin yan sandan Enugu, DSP Daniel Ndukwe, kan lamarin bai kai ga nasara ba domin lambarsa ta ƙi shiga.

Ɗalibar da Ta Kara Makin JAMB Ta Tona Asiri, Ta Yi Bayanin Abinda Ta Aikata Dalla-Dalla

A wani rahoton kuma Ɗalibar Anambra ta yi sabon bayani dalla-dalla kan hanyar da ta bi wajen ƙara yawan makin da ta ci a jarabawar JAMB 2023.

Ejikeme Joy Mmesoma ta shiga kanun labarai kusan mako ɗaya kenan ana kai kawo kan gaskiyar abinda ya haɗa ta da hukumar JAMB.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan PDP Ya Sanar Da Rage Kudin Makaranta Da Kashi 50 A Jami'ar Jiharsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel