Fiqihu: Abubuwan dake jawo wankan Janaba, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Fiqihu: Abubuwan dake jawo wankan Janaba, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malamin ya yi bayanin cikin sauki abubuwan da ya kamata mutum ya sani game da abubuwan da suke faruwa mutum ya bukaci wankan Janaba.

Abubuwan da suke jawo a yi wankan ibada su ne:

1. Fitar maniyyi a cikin bacci, ko a farke, daga namiji ko mace, ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisin da ya ce, “Idan ruwa ya fita a yi wanka.” Wato idan ruwan maniyyi ya fita, a yi wankan janaba.

2. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi, babu wanka a kansa.

3. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, bayan ya farka sai ya ga maniyyi a jikinsa, wajibi ya yi wanka.

4. Idan ya tashi daga barci sai ya ga maniyyi a jikinsa, amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi ya yi wanka, saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa ne yake jawo wanka.

5. Idan mutum ya ga maniyyi a jikin kayansa, amma bai tuna lokacin da ya yi mafarki ba, sai ya yi wanka ya rama sallar da ya yi daga lokacin da ya kwanta wannan baccin da ya yi mafarkin.

6. Saduwa tsakanin mace da namiji, ya shigar da gabansa a cikin gaban mace, wajibi su yi wanka ko da maniyyi bai fito ba, domin Manzon Allah ﷺ Ya ce, “Idan kaciya biyu suka haɗu wanka ya wajaba” ko da maniyyi bai fito ba.

7. Idan mutum ya rungumi matarsa suka yi wasa kawai babu saduwa, kuma maniyyi bai fito ba, babu wanka a kansu, saboda rashin samun dalilan da suke jawowa a yi wanka guda biyu: fitar maniyyi ko shigar kaciyar namiji cikin gaban mace. Idan ba a sami ɗayan biyun ba, babu wanka.

8. Idan maniyyi ya fitowa mutum bayan ya yi wanka, wasu malamai suna ga babu buƙatar ya sake wanka, wankansa na farko ya isa. An ruwaito daga Zuhriy da Hasanul Basriy sun yi fatawa ga wanda maniyyi ya fito masa bayan ya gama wanka cewa babu buƙatar ya sake wanka.

DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya

Fiqihu: Abubuwan dake jawo wankan Janaba, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Fiqihu: Abubuwan dake jawo wankan Janaba, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

9. Idan maniyyi ya fitowa mutum ta hanyar rashin lafiya, ko wata larura, ko aka yi masa wata allura domin a ɗauki maniyyi a jikinsa, duka wannan babu buqatar yin wanka, saboda rashin fitar maniyyi ta hanyar sha'awa.

10. Idan mutum ya ga wani abu a jikinsa, amma yana shakka maniyyi ne ko ba maniyyi ba ne sai ya shinshina. Idan ya sami yaƙini ko zato mai ƙarfi cewa maniyyi ne, sai ya yi wanka domin ya fita daga kokwanto.

11. Haramun ne mutum ya sadu da matarsa tana cikin jinin al'ada ko jinin biƙi, ko ya sadu da ita ta dubura, amma idan ya keta Shari'a ya yi, sai ya yi wanka, kuma ya yi nadama, ya yi kaffara, ya tuba.

12 Abin da yake jawo wanka shi ne ɗaukewar jinin al'ada. Idan mace ta gama jinin al'ada ta tabbatar ya ɗauke har ta ga alamar ɗaukewarsa, sai ta yi wanka kamar yadda ya gabata a baya a wankan ibada.

13. Shi ne jinin biƙi. Idan mace ta haihu, jinin da yake biyo baya ya ɗauke, sai ta yi wanka, kamar yadda ya gabata a wankan ibada.

14. Idan Allah ﷻ Ya arzuta mutum da shiga addinin Musulunci, ya wajaba ya yi wanka na ibada, kamar yadda ya gabata da niyyar ya shigo Musulunci. Saboda wani mutum Ya musulunta, Manzon Allah ﷺ ya umarce shi ya yi wanka.

15. Wankan ranar Juma'a, domin ya je sallah cikin tsarki da tsafta.

16. Idan mutum ya mutu a yi masa wanka kafin a binne shi, sai wanda Shari'a ta ce ba a yi musu wanka, kamar wanda ya yi shahada a filin daga fi sabilillah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel